'Yan Houthi: Mun kama dubban sojojin Saudiyya

'Yan tawaye 'yan Houthi

Asalin hoton, Reuters

A wani abin bazata da ya auku a baya-bayan nan a yakin basasar Yemen, 'yan tawayen kasar 'yan Houthi na cewa sun kashe daruruwan sojojin da Saudiyya ke jagoranta kuma sun kama wasu dubbai daga cikinsu.

Bangarorin biyu sun shafe kwana uku suna musayar wuta a kan iyakokin kasashen biyu, kuma kawo yanzu Saudiyya ba ta ce uffan ba kan batun.

Wani kakakin 'yan tawayen Houthi ya bayyana a tashar talabijin domin yin wannan sanarwar -- inda ya bayyana sojojin a matsayin ma ci amanar kasa.

Daga baya ya sanar da BBC cewa birged uku na dakarun da Saudiyyar ke jagoranta sun mika kansu ga 'yan Houthin a kusa da lardin Najran na Saudiyya, kuma ya ce 'yan tawayen sun kwace makamai da motocin yaki masu yawa daga hannunsu.

Kakakin ya kuma ce sojojin da suka kama sun fito ne daga kasashe daban daban, kuma za su nuna wa duniya su a talabijin ranar Lahadin.

Saudiyya ba ta ce uffan ba game da wannan ikirarin na 'yan Houthi -- kuma kawo yanzu babu wanda ya iya tabbatar da sahihancinsu.

Amma idan bayanin ya tabbata, to lallai wannan zai kasance mai mummunan tasiri ga Saudiyya -- wanda makonni kadan kenan da wasu hare-haren da aka kai mata a wasu matatun man fetur inda hakan ya janyo gagarumar asara ga tattalin arzikinta, kuma matakin ya janyo hauhawar farashin mai a kasuwannin duniya.

'Yan Houthi sun ce su ne suka kai wadancan hare-haren, amma Saudiyya ta kafe cewa Iran ce ke da alhakin kai hare-haren.

A 'yan watannin da suka gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta kara kaimi wajen kawo karshen yakin da kawo yanzu an kiyasta ya yi sanadiyar mutuwar mutum 70,000.