Hotuna: Yadda harin da Saudiyya ke jagoranta ya kashe mutum 100 a Yemen

Fiye da mutum 100 ne suka mutu a Yemen bayan da rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta ta kaddamar da wasu jerin hare-haren sama a wani wajen da ake tsare da mutane, a cewar kungiyar agaji ta kasa da kasa wato International Committee of the Red Cross (ICRC).

Yemen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ICRC ta ce a kalla wadanda suka tsira daga harin 40 ne suke karbar taimakon gaggawa a asibitin da ke birnin Dhamar.
Red Crescent medics walk next to bags containing the bodies of victims of Saudi-led airstrikes on a Houthi detention centre in Dhamar, Yemen,

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jami'an ICRC sun jera jakar gawa da ke dauke da gawarwakin mutanen da harin ya kashe.
Yemen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta wadda ke goyon bayan Yemen, ta ce harinta ya lalata wani jirgi marar matuki da kuma wajen da ake ajiyar makami mai linzami.
Yemen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban tawagar ICRC a Yemen Franz Rauchenstein, ya ce ma'aikatan kungiyar sun yi ta tattara gawarwakin a wajen tare da bayyana cewa zai yi wuya a samu masu rai a karkashin baraguzan.
Yemen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazauna yankin sun ce sun ji hare-haren sama wajen guda shida ranar Lahadi da daddare.
Yemen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyar 'yan tawaye ta Houthi da Iran ke goyon baya ta ce harin ya shafi wani wajen da ta mayar gidan yari. ICRC ta ce ta taba ziyartar mutanen da ake tsare da su a wajen.

Tun shekarar 2015 Yemen ke cikin yaki, lokacin da mayakan Houthi suka turasasa wa Shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi da ministocinsa tserewa daga babban birnin Yemen Sanaa.

Saudiyya na goyon bayan Shugaba Hadi, ta kuma jagoranci gamayyar rundunar hadaka don kai hare-haren sama kan 'yan tawayen Houthin.

Gamayyar rundunar hadakan tana kaddamar da hare-haren sama kusan kowace rana, yayin da mayakan Houthi suka fi mayar da hankali kan harba makamai masu linzami Saudiyya.

Yakin basasar ya jawo kasar ta shiga mummunan yanayi, inda kashi 80% na al'ummar kasar - fiye da mutum miliyan 24 - na bukatar agajin gaggawa na kariya, da suka hada da mutum miliyan 10 da suka dogara da abincin agaji da ake kai musu don su ci su rayu.

An yi amannar cewa fiye da mutum 70,000 sun mutu tun shekarar 2016 sakamakon rikicin, a cewar kiyasin Majalisar Dinkin Duniya.