Hotuna: Yadda harin da Saudiyya ke jagoranta ya kashe mutum 100 a Yemen

Fiye da mutum 100 ne suka mutu a Yemen bayan da rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta ta kaddamar da wasu jerin hare-haren sama a wani wajen da ake tsare da mutane, a cewar kungiyar agaji ta kasa da kasa wato International Committee of the Red Cross (ICRC).

Tun shekarar 2015 Yemen ke cikin yaki, lokacin da mayakan Houthi suka turasasa wa Shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi da ministocinsa tserewa daga babban birnin Yemen Sanaa.

Saudiyya na goyon bayan Shugaba Hadi, ta kuma jagoranci gamayyar rundunar hadaka don kai hare-haren sama kan 'yan tawayen Houthin.

Gamayyar rundunar hadakan tana kaddamar da hare-haren sama kusan kowace rana, yayin da mayakan Houthi suka fi mayar da hankali kan harba makamai masu linzami Saudiyya.

Yakin basasar ya jawo kasar ta shiga mummunan yanayi, inda kashi 80% na al'ummar kasar - fiye da mutum miliyan 24 - na bukatar agajin gaggawa na kariya, da suka hada da mutum miliyan 10 da suka dogara da abincin agaji da ake kai musu don su ci su rayu.

An yi amannar cewa fiye da mutum 70,000 sun mutu tun shekarar 2016 sakamakon rikicin, a cewar kiyasin Majalisar Dinkin Duniya.