Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsintsiyar APC na neman wargajewa a jihar Kano
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, rikicin da ya biyo bayan zaben shugabannin jam`iyyar APC na jihar ya kara jika, bayan kwamitin sauraron korafin zabe ya fayyace bangaren da zai saurari koke-kokensa.
Bangarori biyu ne dai suka yi zabe a Kano, wato da tsagin gwamna Ganduje da kuma tsagin senata Ibrahim Shekarau.
Amma kwamitin sauraron korafin, wanda hedikwatar jam`iyyar APC ta kasa ta tura jihar ya ce bangaren da suka yi zabe a filin wasa na Sani Abatcha ne kadai zai saurara, inda tsagin gwamna Ganduje ya yi nasa zaben.
Sai dai tsagin shekarau ya ce ko a jikinsa, saboda zaben da ya yi shi ne sahihi.
Kwamitin sauraron korafin zaben wanda mista Tony Macfoy ke jagoranta ya bayyana cewa yana aikin ne da umurnin uwar jam`iyyar APC, don haka albasar sautu ba a yanke mata ganye, ba shi da da hurumin sauraron korafin kowa face bangaren da ya yi zabe a filin wasa na Sani Abatcha da ke Kano, wato inda tsagin gwamna Ganduje ya gudanar da nasa zaben.
Dr Aminu Waziri dan kwamitin sauraron korafin ne, ya ce duk wanda abin bai masa dadi ba, Indai har ya bi ka'idojin da kundin tsarin mulkin APC ya tanada, na neman wasu mukamai za su saurare su a kuma share musu hawaye.
''Za mu saurari wadanda suka gudanar da zabe a filin wasa na Sani Abatcha da ke kano, idan aka ce mu tattaru a wannan daki kai kuma ka fice ka yi a wani wuri na daban, ai ba ka cikin wadanda suke da karsashin abin da ya faru a dakin,'' in ji shi.
Duk da cewa bangarori biyu da suka yi wannan zabe duka suna ikirarin cewa hedikwatar APC ta kasa ta saka musu albarka kuma da amincewarta suka gudanar da zaben, wannan alkibla da kwamitin sauraron kwarafin zaben jam`iyyar APCn ya sa a gaba, ta sa wasu na ganin cewa hediwatar jam`iyyar a fakaice ta yi na`am da bangaren gwamna Ganduje Kenan.
Amma tsagin tsohon gwamnan jihar Kano, Senata Ibrahim Shekarau mai wadansu jiga-jigan APC bakwai, ya ce kan mutanensa a hade yake kuma bas u da korafi ballantana su bukaci mai share musu hawaye don haka can ga su gada, wai zomo ya ji kidan farauta.
Honarabul Sha`aban Sharada jigo ne daga cikin jiga-jigana ce wannan sun zo karbar korafi amma su ba su da korafi sun gudanar da zabe halattace, kuma sun zabi Alhaji Haruna Zago, an yi hakan ne tare da ragowar sauran jiga-jigan jam'iyyar APC maza da mata.
Wannan ja-ni-in-ja-kan da ake yi a jam`iyyar APC mai alamar tsintsinya a jihar Kano, ko shakka babu na nuna cewa tsintsiyar ta kama hanyar kuncewa, kuma lamarin ka iya munana idan ta kunce, saboda `yan Magana kan ce tsintsiyar da ba ta da dauri ba ta shara.
Wannan ne ma ya sa wasu magoya bayan jam`iyyar ke ganin cewa karkata kwamitin sauraron korafin ga wani bangare kadai ba za ta magance matsalar ba, sai Uwar jam`iyyar APCn da daina noke-noke, ta hada da lalama ko tausa ga bangaren da ya dace, kasancewar jihar Kano rumbu ce ta miliyoyin kuri`u, ga shi har an fara kada gangar zaben 2023.
Amma wasu kuma na ganin cewa jam`iyyar ta san abin da da ta taka saboda wanda ya daure kura shi ya san yadda zai kwance ta.