Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir ya rasu

Asalin hoton, Gaya Emirate
Allah Ya yi wa Sarkin Gaya a jihar Kano Alhaji Ibrahim Abdulkadir rasuwa a ranar Laraba.
Mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar wa BBC da rasuwar, amma ta ce sai nan gaba kadan za ta fitar da sanarwar a hukumance bayan sakataren gwamnatin jihar ya isa Gayan.
Sarki Ibrahim Abdulkadir ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Sarkin ya rasu yana da shekara 91, kuma ya shafe shekara 30 yana kan karagar mulki.
A shekarar 2020 ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da Sarkin Gaya mai daraja ta farko, tare da na wasu masaratun uku a jihar Kano.
An yi jana'izar Sarkin ne da misalin karfe 4 na yammacin Laraba a babban masallacin Juma'a na Gaya.
An kuma binne shi a hubbaren da ke cikin gidan Sarkin Gaya.











