Matasan da suka yada hotunan tsiraicin wata budurwa a Sokoto za su sha dauri

Wata Babbar Kotun Majistare a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta nemi wasu matasa uku, da suka naɗi bidiyon tsiraicin wata matashiya sannan suka yaɗa a shafukan sada zumunta, su biya ta diyyar naira dubu ɗari uku.

Ranar Litinin ne kotun ta samu matasan, Umar Abubakar da Mas'ud Abubakar Giɗaɗo da kuma Aminu Hayatu Tafida da laifi kan tuhuma uku, kuma ta yanke masu hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi kowannensu a gidan yari ko kuma zaɓin tara ta naira dubu ɗari huɗu kowanne.

Mahaifiyar matashiyar ta ce sun kwashe sama da shekara ɗaya suna faɗi-tashi don neman haƙƙin 'yarsu.

Lamarin shi ne ya zama silar fasa auren matashiyar, wadda aka sanya wa rana a lokacin.

Mahaifiyar matashiyar ta ce sun ce sun yi farin ciki da wannan hukunci na kotu kuma suna ganin ya yi dai-dai da laifin da matasan suka aikata.

"Abu ne da kusan shekara ɗaya muna ta abu guda, yanzu an zo ƙarshe kuma hukuncin ya yi min daɗi," a cewarta.

Ta bayyana wa BBC cewa da ba ta jajirce ba da ba a kai ga haka ba saboda ta fuskanci matsaloli da faɗi tashi da dama a yayin da ake shari'ar.

"Na sha matsin lamba sosai dangane da wannan shari'a, har da tsakar dare an shigo gidana don a tsorata ni. Na gaya wa hukumar 'yan sanda kuma sun tabbatar ba sata aka zo a yi min ba.

"Har ofishin Antoni-Janar aka kira ni, wasu baristoci biyu suka ajiye ni amma babu wani bayani mai kwari da suka yi. Haka dai, yau a ce ana nema na a can gobe a ce in je can kuma ina zuwa, daga karshe babu wani abu da ya fito.

"Na yi tsaye na ƙi yarda. Tun da an zalunce ni ne, sai da na bi haƙƙina. Da na biye masu da watakila na janye karar," a cewar mahaifiyar.

Mahaifiyar matsahiyar ta bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru 'yarta ta shiga tsananin damuwa.

Dama ana shirin yin bikinta a lokacin da suka fitar da hoton nata a shafukan sada zumunta, don haka mijin da za ta aura sai ya janye, ya ce ya fasa auren.

Ta ce "Sai da na je na kai ta asibiti saboda kullum tana cikin damuwa, ta samu matsala da kwakwalwarta a lokacin, ko da yaushe tana cikin rashin lafiya. Kuma ta sha cewa ita kawai so take a bi mata hakkinta, ko a gaban alkali ma ta bayyana haka."

Mahaifiyar ta bayyana cewa a yanzu 'yarta ta yi aure watan da ya wuce da wani mijin kuma ta samu kwanciyar hankali tun da an yanke hukuncin da ya dace ga mutanen da suka ci zarafinta.

A bara ne Hukumar Hisbah a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da kama matasan uku bisa zarginsu da yaɗa bidiyon matashiyar mai shekarar 20 wadda ɗaya daga cikinsu ya yi lalata da ita.

Kwamandan hukumar Hisbah Dr. Adamu Bello Asarawa ya shaida wa BBC cewa mahaifiyar yarinyar ta kai ƙorafi inda ta ce tun a shekarar 2017 matasan suka lalata yarinyar tare da ɗaukar bidiyon.

Me ya sa yaron ya ɗauki bidiyon?

Kwamandan hukumar Hisbah ya ce yaron bai bayar da wasu dalilai da suka sa ya ɗauki bidiyon tare ya yaɗawa ba.

''Ɓarna dai ta riga ta faru. Rashin tarbiyya ce irin ta yara. Ina ga ya yi hakan ne don cin zarafi da lalata mata rayuwa da kuma suna,'' in ji Dr Adamu.

Kwamandan ya ce sun tambayi yaron ko zai auri matashiyar ne tun da yanzu ya lalata maganar aurenta, ''sai ya ce min ba shi da niyyar hakan, ai ba zai iya aurenta ba don dama da niyyar yaudara ya je,'' in ji shi.

Shekarun yaron 17 ita kuma yarinyar tana da 16 a lokacin da lamarin ya faru. A yanzu kuma yaron na da shekara 20 ita kuma 19 a cewar shugaban Hisbar.

''Dukkansu yara ne lokacin da abin ya faru don ba wanda ya kai 20," in ji shi.