'Yan adawa sun goyi bayan juyin Mulki a Guinea

Sojojin Guinea

Asalin hoton, AFP

Wata gamayyar jam'iyyun adawa a Guinea ta ayyana goyon bayanta ga jagororin juyin mulkin da suka kwace mulki daga Shugaba Alpha Conde a ranar 5 ga Satumba, kamar yadda wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta ediaguinee ta ruwaito.

Kungiyar National Alliance for a Democratic Alternative (ANAD) a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ta ce za ta goyi bayan juyin mulkin "don gina dimokuradiyya mai dorewa a ƙasar."

ANAD gamayyar jam'iyyun siyasa 14 ce a kasar, ciki har da babbar jam'iyyar kasar ta Union of Democratic Forces of Guinea (UFDG) wacce Cellou Dalein Diallo ke jagoranta.

Diallo, wanda ya karanta sanarwar a madadin ANAD, ya ce hamɓarar da Shugaba Conde "wata babbar dama ce ta girmama dukkan 'yan Guinea da suka ba da gudunmawarsu wajen faɗuwar gwamnatin kama-karya."

Diallo ya kalubalanci Conde a zaɓen shugaban kasa mai cike da ce-ce-ku-ce da aka gudanar a bara, kuma ya ci gaba da cewa shi ya yi nasara.

Sai dai sojojin juyin mulkin sun gaza sakin fursunonin siyasa kamar yadda suka yi alkawari.

Shafin yaɗa labarai na intanet na Africaguinee ya ruwaito cewa dakarun tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye ga magoya bayan da suka taru a babban birnin ƙasar Conakry, suna jiran a saki fursunonin.

Mafi yawan wadanda aka ɗaure din magoya baya da jami'an gamayyar kungiyoyin fararen hula da jami'iyyun siyasa na FNDC ne, da suka jagoranci wasu jerin zanga-zanga na tsawon shekara guda a 2020, don nuna adawa da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin da Shugaba Conde ya yi don ya samu tazarce a karo na uku.

________________________________________

Sojoji za su gana da 'yan siyasa

President Alpha Condé has not been seen in public since he was captured on Sunday

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ba a ga Shugaba Alpha Condé a bainar jama'a ba tun bayan da aka kama shi ranar Lahadi

Shafin yada labarai na intanet na Mediaguinee a ranar Litinin ya ce sabbin hukumomin sojin za su gana da dukkan jagororin siyasa don tattaunawa "nan gaba kadan."

Shafin Mediaguinee ya ce "sabbin shugabannin kasar ne suka tabbatar mata da batun."

Sai dai ba a fadi ranar yin taron ba, sannan ba a bayyana wadanda za su halarta ba.

A ranar Litinin jagoran juyin mulkin Kanal Mamady Doumbouya, ya gana da jami'an gwamnatin da aka hamɓarar wadanda aka kwace fasfunansu da kuma motocinsu da gwamnati ta ba su.

Kanal Doumbouya ya kuma bai wa dakarun da ke kare shugaban kasa umarnin su bar Conakry "ba tare da bata lokaci ba ko su fuskanci hukunci," a cewar wata kafar yada labarai ta Visionguinee.

Ya ce: "Mun bai wa masu tsaron tsohon shugaban kasa umarnin su hadu da Rundunar Kar-ta-kwana da ke da nisan kilomita 36 daga wajen birnin. Idan suka ki yin hakan kuma, za a kakkabe su a faɗin ƙasar ta hanyar bin doka."

Kafafen yaɗa labaran Guinea sun ce an kashe wani mai tsaron fadar shugaban kasa a yayin musayar wuta da 'yan rundunar Kanal Doumbouya, a kusa da fadar shugaban ranar 5 ga Satumba yayin juyin mulkin.

Rahotanni sun ce har yanzu ba a san yawan wadanda suka mutu ko suka jikkata ba a yayin juyin mulkin.

________________________________________

An sassauta dokar hana fita

Sojojin juyin mulkin sun sassauta dokar hana fitar da suka saka inda ta koma daga karfe 10 na dare agogon GMT zuwa karfe 4 na asuba agogon GMT.

Rahotanni sun ce an dauki matakin ne a kokarin girmama dokokin da ake dauka na hana yaduwar cutar Covid-19.

Da farko sojojin sun sanya dokar hana fitar ne tun daga karfe 8 na dare.

Guinea

A ranar Litinin ne jagoran juyin mulkin Kanal Mamady Doumbouya, ya sanar da ɗage dokar hana fitar a yankunan da ake hakar ma'adinai.

"A don haka ne, muka ba da umarnin a bar iyakokin ruwa a buɗe don ci gaba da fitar da ma'adinan da aka haka," in ji shi.

Guinea ita ce kasa ta biyu da ta fi kowacce fitar da ma'adanin bautixe wanda ake alminiyom da shi. Ita ce ke bai wa China ma'adanin.

Rahotanni sun ce Rasha ta umarci jagororin juyin mulki su saki Shugaba Conde. Kamfanin Rasha na alminiyom ya yi barazanar janye ma'aikatansa daga Guinea saboda halin da kasar ta shiga na rashin tabbas.

________________________________________