Afghanistan: Ana cike da fargabar hari a filin jirgin saman Kabul

Sama da mutane 82,000 aka kwashe tun bayan da Taliban ta karbe iko da kasar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sama da mutane 82,000 aka kwashe tun bayan da Taliban ta karbe iko da kasar

Wasu kasashe da dama sun ce akwai babbar barazanar kai harin ta'addanci a filin jirgin saman Kabul, a don haka suka gargadi 'yan kasarsu da kada su ze can.

Kasashen Australia da Amurka da Burtaniya sun gargadi mutanensu da suka riga suka je filin, amma suna waje da su bar wajen ba tare da bata lokaci ba.

An yi gargadin ne yayin da ake ganin wata kungiya mai alaka da ISIS na barazanar kai hari filin jirgin saman, yayin da dubban jama'a ke tururuwa domin neman ficewa daga kasar da ta fada hannun Taliban, bayan fara ficewar sojojin Amurka da ke kan wa'adin karshen watan nan;

Yayin da ake aikin ci gaba da kwashe 'yan kasashen wajen, inda zuwa yanau aka raba sama da 82,000 da Afghanistan din ta filin jirgin saman na Kabul, bayan da birnin ya fada hannun Taliban kwana goma baya, wannan fargaba ta kai hari kan filin jirgin na karuwa ne kamar yadda kasashen da suka fitar da gargadin ke gani.

Inda kungiyar da shugaba Biden ya yi wa lakabi da ISIS-K, wadda ke da alaka da ISIS, wadda kuma babbar abokiyar gabar 'yan Taliban ce ake ganin za ta iya kai hari filin jirgin saman ko da kuwa na kunar bakin-wake ne.

Kasashe na kokarin kammala kwashe jama'a zuwa karshen 31 ga watan nan na Agusta

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kasashe na kokarin kammala kwashe jama'a zuwa karshen 31 ga watan nan na Agusta

Ganin yadda dubban jama'a ke tattare a can, yayin da Amurka ke kokarin cimma wa'adin zuwa ranar 31 ga watan Agustan nan domin kwashe dakarunta da sauran na kasashe kawaye.

Ministar harkkin wajen Australia, Marise Payne, ta ce akwai babbar barazanar kai hari ta 'yan ta'adda a yanzu haka.

Bayanin da ta yi 'yan sa'o'i bayan da Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gaya wa wadanda ke jira a sassan filin jirgin saman na Kabul da su gaggauta barin inda suke.

Ita ma Burtaniya ta fitar da irin wannan shawara, tana kira ga jama'a da su je wani wuri mafi kwanciyar hankali su jira sanarwa ta gaba.

A yayin wani jawabi a ranar Talata shugaban Amurka Joe Biden ya ce dole ne a kawo karshen aikin kwashe mutanen da kasarsa ke jagoranta ba da jimawa ba saboda karuwar barazanar hari daga kungiyar ISIS a Afghanistan.

Babu wata kasa daga cikin dukkanin wadannan kasashe da suka ankarar game da barazanar harin, da ta bayar da karin bayani game da harin da suke ganin za a kai.

Sauran kasashen kawancen dai sun bukaci kara wa'adin, abin da shugaba Biden ya ce babu bukatar hakan, a yanzu, kamar yadda ita ma Taliban ta nuna kin yarda da karin.

Antoni Blinken ya ce Amurka na kokarin kwashe 'yan Afghanistan da dama da za ta iya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Antoni Blinken ya ce Amurka na kokarin kwashe 'yan Afghanistan da dama da za ta iya

Sai dai kungiyar ta yi alkawarin bayar da damar ci gaba da aikin kwashe bakin 'yan kasashen waje da 'yan Afghanistan, har bayan wa'adin na 31 ga wata, kamar yadda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antoni Blinken ya fada.

Sakataren a ranar Laraba ya ce kusan mutum 19,000 aka kwashe a cikin sa'a 24 da ta gabata, kuma an kara azama a aikin.

Kuma za a iya kamala aikin zuwa karshen watan na Agusta.

Ya kara da cewa akwai 'yan Amurka kusan 1,500 a kasar ta Afghanistan kuma gwamnatinsu na kokari haikan domin gano inda suke.

Hukumar liken asiri ta Amurkar CIA da hukumar sojin Amurkar na amfani da jirage masu saukar ungulu da sojojin kasa, domin zakulo wadannan Amurka su fitar da su daga kasar, kamar yanda Amurkar da wasu jami'ai suka sheda wa jaridar Wall Street Journal.

Ma'aikatar tsaro ta Amurka ta ce akwai mutane 10,000 da suke jiran a kwashe su daga filin jirgin Kabul.

Ana kuma fargabar cewa akwai dubban 'yan Afghanistan da fafur-fafur suke son ficewa amma ba za su iya kaiwa ga filin jirgin saman ba.

Wakiliyar BBC ta ce da dama daga cikin wadanda 'yan Taliban suke hanawa shiga filin jirgin suke korarsu su koma suna da takardun tafiya.

Burtaniya a nata bangaren ta ce aikin kwashe 'yan kasarta na tafiya sosai, inda ta fitar da 1,200 a ranar Laraba

Sakataren harkokin wajen kasar Dominic Raab y ace gwamnatinsa za ta yi amfani da duk wata sa'a da rana da suka rage ta fitar da 'yan Burtaniya da kuma 'yan Afghanistan da suka cancanta.

A yanzu dai akwai sojojin Amurka 5,800 da na Burtaniya 1,000 da ke aikin kare filin jirgin saman na Kabul.