Afghanistan: Ya girman noman ganyen opium da ribarsa ga Taliban?

Poppy cultivation

Asalin hoton, Getty Images

Taliban ta yi iƙirarin cewa an daina noman ganyen opium kuma an dakatar da shigar da haramtatun kwayoyin zamanin mulkinta na baya a Afghanistan.

Duk da cewa an samu raguwa sosai a 2001 - lokacin da ta yi mulkin ƙasar a baya - noman ganyen opium a yankunan da Taliban ke riƙe da su ya ƙaru a shekarun baya-bayan nan.

Mene ne yawan ganyen opium da ake nomawa a Afghanistan?

Noman opium na ɗaya daga cikin ganyayyakin da ake amfani da su wajen haɗa kwayoyin maye, ciki har da hodar iblis.

Afghanistan ita ke kan gaba wajen noma ganyen opium a duniya, a cewar ofishin hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yakar shan kwayoyi.

Afghanistan ke samar da kashi 80 cikin dari na opium a duniya.

A 2018 Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa noman ganyen opium shi ke sama wa ƙasar kashi 11 cikin 100 na ƙudaden shiga.

Alkalumma

Me Taliban ta ce za ta yi kan opium?

Bayan Taliban ta sake karbe ikon Afghanistan, kakakinta Zabuhullah Mujahid ya ce: "Lokacin da muke mulki ba a samar da kwayoyi."

Ya ce "za mu kawo karshen noman opium baki ɗaya" sannan za a daina fasa kwaurinsa.

Ya girman nomansa zamanin Taliban?

A farko, noman ganyen opium din ya ƙaru a ƙarƙashin mulkin Taliban - daga kadada 41,000 a 1998 zuwa 64,000 a 2000, a cewar bayanan ma'aikatar cikin gida ta Amurka.

Noman galibi ya kasance a ƙarƙashin yankin da Taliban ke mulka na Helmand, wanda ke samar da kashi 39 cikin 100 na ganyen da ake nomawa a duniya baki ɗaya.

Amma a watan Yulin 2000 Taliban ta haramta noman opium a yankuna da dama da take mulka.

Kuma wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a Mayun 2001 "ya lura da nasarar da ake samu na haramta noman a yankunan bakin ɗaya da Taliban ke iko".

Bayan haramcin Taliban kan noman wannan ganyen, an lura da ragin da aka samu wajen fitar da hodar iblis a duniya tsakanin 2001 zuwa 2002.

Sai dai, daga baya abubuwa sun sauya.

Duk da cewa an ci gaba da wannan noma a yankunan da Taliban ke mulka kafin kifar da gwamnati, yawanci ana noman wannan ganyen ne a yankuna da Taliban ke iko.

Yankin Helmand a kudancin Afghanistan, misali, ya fi girman gonaki da ake amfani da su wajen noma opium a 2020 lokacin da Taliban ke rike da shi.

Ya Taliban ke samun kudi daga noman?

Noman opium na kan gaba wajen samar da aikin yi a Afghanistan, a 2019 noman opium na samar da aiki ga yan kasar 120,000, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

Taliban na samun riba ta kudaden harajin da ake samu daga noman opium da sararafawa da kuma fatauci, a cewar ma'aikatar cikin gida ta Amurka.

Suna karbar harajin kashi 10 cikin 100 na kudaden noman opium a gonaki.

Opium harvest

Asalin hoton, Getty Images

Ana kuma karɓar kuɗaɗen haraji daga dakunan kimiyar da ake sarafa ganyen opium zuwa hodar iblis, da kuma masu fataucin kwayar.

Kudaden da Taliban ke samu a kowacce shekara daga wannan harkar na kai wa daga dala miliyan 100 zuwa miliyan 400.

Kwayar ke samarwa Taliban kashi 60 cikin 100 na kudaden shigarta a shekara, a cewar Amurka.

Sai dai akwai wasu ƙwararru da suke da ja kan waɗannan alkaluma.

David Mansfield, wani mai bincike kan migayun kwayoyi, ya ce: Harajin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka ke magana akai ba a gani a kasa - kuma ba a ganin tasirin haka ga fanin hada-hadar kudade.

"Ya ce watakila kuɗaɗen da suke samu ba zai haura dala miliyan 40 ba."

A ina aka fi shigar da ƙwayoyin?

Kashi 95 cikin 100 na hodar iblis din da ake samarwa daga Afghanistan ana shigar da su kasuwannin Turai.

Ko da yake, kashi 1 bisa 100 na hodar iblis din Afghanistan ke shiga Amurka, a cewar hukumar da ke yaki da migayun kwayoyi ta Amurka. Akasari daga Mexico ake kai musu.

Tsakanin 2017 zuwa 2020, sama da kashi 90 cikin 100 na kwayoyin ake safararsu ta hanya.

Amma a yan kwanakin nan ana samun karuwar kama masu safarar hodar a teku da ta hada Indiya da Turai.

Duk da cewa ana samun sauye-sauye, noman opium da kwace duk wani abu da aka samar ta ganye ya karu a cikin sama da shekaru 20 a Afghanistan.

Kwace irin wadanan kwayoyi ya yi matsakaicin tasiri kan kasar da ayyukan noma ganyen.

A 2019 kudaden shigar da ake samu ta wannan hanyar ya yi kasa da kashi 8 cikin 100.

Presentational grey line
Reality Check branding