Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Trippier, Haaland, Icardi, Griezmann, Origi, Dzeko, Cunha

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran gwada lafiyar Lionel Messi mai shekara 34, ranar Litinin, kafin kammala komawar dan gaban na Argentina, wanda ya raba gari da Barcelona, bayan kwantiraginsa ya kare, Paris St-Germain. (Jaridar L'Equipe)
A cikin kwanakin da ke tafe ne za a gabatar da Messi a matsayin dan wasan PSG, a wani biki na musamman da za a yi a Eiffel Tower, da ke birnin Paris. (ESPN)
Sai dai Barcelona na kokarin hana duk wani yunkuri na sayen Messi da PSG za ta yi, ta hanyar gabatar da korafi ga Hukumar Turai, da cewa kungiyar ta Faransa za ta saba ka'idar kashe kudinta idan har ta yi nasarar sayen dan wasan na Argentina. (Jaridar Marca)
Tottenham na daga cikin kungiyoyin da suka yi kokarin daukar Messi bayan da Barca ta ce ba zai ci gaba da zama a Nou Camp ba. (Jaridar Express)
A shirye Arsenal take ta shiga zawarcin dan bayan Atletico Madrid Kieran Trippier bayan da Manchester United ta kasa daidaitawa da dan tawagar Ingilar mai shekara 30, da zakarun Sifaniyar. (Jaridar Sun)
Kociyan Roma Jose Mourinho na sha'awar daukar dan gaban Paris St-Germain, dan Argentina Mauro Icardi, mai shekara 28, ganin cewa dan Bosnia, Edin Dzeko, mai shekara 35, na son tafiya Inter Milan. (Jaridar Gazzetta dello Sport)

Asalin hoton, Getty Images
Dzeko na dab da tafiya San Siro a matsayin wanda zai maye gurbin dan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 28, wanda shi kuma ke dab da sake komawa Chelsea. (Jaridar Sun)
Arsenal na gogayya da abokiyar hamayyarta ta arewacin London Tottenham wajen zawarcin dan gaban Fiorentina, dan Serbia Dusan Vlahovic, inda Spurs din ke son dan wasan na Serbia mai shekara 21 domin maye gurbin Harry Kane, wanda shi kuma Manchester City ke matukar so. (Tashar Sky Sport)
Southampton na kokarin sake sayen dan wasan tsakiya na Liverpool, Alex Oxlade-Chamberlain, dan Ingila mai shekara 27, bayan shekara 10 da barin kungiyar ta St Mary. (Jaridar Sun)
Daraktan wasanni na Bayern Munich Hasan Salihamidzic ya tabbatar da cewa kungiyar ta Jamus na sha'awar sayen dan gaban abokan hamayyarsu Borussia Dortmund, wato Erling Braut Haaland, dan Norway mai shekara 21. (Goal)

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na shirin taya dan gaban Barcelona na Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 30. (Todofichajes)
Bayanai na danganta Porto da West Ham da Leeds da kuma Norwich da matashin dan wasan tsakiya na Fulham, dan Ingila Fabio Carvalho, mai shekara 18, wanda ya ki yarda ya kara tsawon kwantaraginsa da kungiyar. (Jaridar Mail)
Mai yiwuwa Leicester City ta fara zawarcin dan bayan Southampton Jannik Vestergaard, mai shekara 29, a matsayin wanda zai maye gurbin Wesley Fofana, wanda ya ji rauni. Ita ma West Ham an ce tana son dan bayan, dan Denmark.(Talksport)

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Leeds United na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Hertha Berlin Matheus Cunha, mai shekara 22, wanda ya ci lambar zinare ta gasar Olympic da tawagar Brazil aTokyo ranar Asabar. (Jaridar Star)
Ita ma kungiyar Atalanta an ce tana sha'awar Cunha, wanda Hertha ta kara farashinsa zuwa kusan fam miliyan 25 bayan nasarar da Brazil ta samu a Japan. (Jaridar Calciomercato)
Bayanai na danganta Burnley da dan wasan gefe na Santos, dan Brazil Arthur Gomes mai shekara 23, wanda a yanzu yake zaman aro a Atletico Goianiense. (Jaridar Burnley Express)
Barcelona ta yi tayin bayar da golanta Neto, mai shekara 32, ga kungiyoyin arewacin London Arsenal da Tottenham. (Jaridar Express)
West Ham ta fara tattaunawa da Divock Origin na Liverpool, dan Belgium mai shekara 26. (Jaridar Football Insider)











