Lionel Messi ya fashe da kuka yayin bankwana da Barcelona

Lokacin karatu: Minti 4

Cikin kuka da share hawaye, Lionel Messi ya ce komawarsa Paris St-Germain "abu ne mai yiwuwa amma ba a cimma yarjejeniya ba" yayin da yake tabbatar da barinsa Barcelona ranar Lahadi.

Messi ya kawo ƙarshen zamansa na shekara 21 a Barca, wadda ta ce ba za ta iya cika alƙawarin da ta yi masa ba na yarjejeniyar da suka ƙulla saboda dokokin hukumar La Liga na biyan albashi.

Ɗan wasan mai shekara 34 ya fashe da kuka yayin jawabinsa na bankwana da Barcelona.

Yanzu haka Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon duniya sau shida ba shi da ƙungiya kuma duk kulob ɗin da ke son sa kyauta zai ɗauke shi.

Ya buga wasa 778 tare da jefa kwallo 627 a raga, inda ya lashe kofin La Liga 10 da kofin zakarun nahiyar Turai hudu sai kofin zakarun duniya uku, duka dai ya lashe kofina 35 a zamansa.

Tun kafin ɗan wasan ya fara magana ya fashe da kuka lokacin da yake hawa dandamalin mahalarta taron suka fara masa tafi.

Messi ya fara da cewa "Gaskiya ban san da mai zan fara ba, ban kuma san me zan ce ba. Duk kwana kin nan babu abin da nake sai tunanin mai zan faɗa a wannan rana.

"Yanayi ne na tashin hankali bayan kwashe shekaru masu yawa anan, kusan duka rayuwata kenan. Ban shirya tunkarar hakan ba.

"A bara da ake ta rikicin tafiya ta na shirya abin da zan faɗa amma a yau kwata-kwata ba ni da abin faɗa. Ni da iyali na mun gama sakin jiki cewa muna gida," in ji Messi.

'Ban taɓa tsammanin zan iya yin bankwana ba'

Messi ya ce bayan shekara 21 yanzu zai tafi da 'ya'yansa uku masu ruwa biyu yan Argentina da kuma jinin Cataloniya a jikinsu. Mun daɗe a nan, nan ne gidanmu. Ina farin ciki da zama na anan, duka abokan kwallona da muka yi wasa tare.

"Na yi wa Barcelona duk abin da zan iya tun daga ranata ta farko har zuwa ta ƙarshe. Ban taɓa zaton ranar bankwana za ta zo ba."

Duk da kwashe kusan shekara guda da ake yin wasa ba tare da 'yan kallo ba Messi ya ce ya so a ce ya yi bankwana da magoya bayan da suke cika filin wasa na Camp Nou saboda su.

'Ina sa ran wataran zan dawo'

Mun fuskanci matsi a lokuta da dama, a wasu lokutan kuma munyi murna da farin ciki, amma kaunar da mutane ke mani ba ta taɓa sauya wa ba.

"Ina fatan wata rana zan dawo in kasance cikin tawagar wannan kungiya a wani lokaci, ta ko yaya domin dai mu kara mayar da kungiyar wacce tafi ko wacce a duniya.

"Na manta abubuwa da dama da na so faɗa, amma wannan dai zan iya fadi yanzu. na yi tunanin fadin abubuwa da dama amma kalmomin sun ƙi zuwa. Ina godiya ga kowa."

'Barcelona ta gaza'

An tambayi Messi mai zai iya ƙarawa game da barinsa Barcelona, sai yace "A fili yake na yi wa Barcelona komai, amma sun gaza yi mani abin da nayi mata saboda La Liga.

"An ta fadin abubuwa da dama a kaina, amma a ta ɓangarena na yi duk abin da zan iya domin na ci gaba da zama a kungiyar.

"A shekarar da ta gabata ban so zama ba, amma haka na tsaya. Amma wannan shekarar na so zaman amma ba zan samu hakan ba."

Lokacin da Messi zai sauka daga dandamalin da ya gabatar da bayaninsa an kara ruɗewa da tafi a karo na biyu.

Barin sa abu ne mai taɓa zuciya wanda ba a yi zatonsa ba, hatta Messi da kansa bai taɓa tsammanin hakan za ta faru ba gare shi.

"Babu ɗan wasan da a duniya ya taɓa yi wa ƙungiyarsa abin da ya yi"

Man yan masu sharhi a fagen wasanni da masu sha'awar wasanni sun fara bayyana ra'ayoyinsu ganin wannan abin da ya faru mai cike da sosa zuciya.

Gary Lineker tsohon dan wasan gaban Barcelona ne, wanda ya yi shuhura a yanzu wajen gabatar da shirye-shiryen wasanni a tashohin talabijin irinsu BBC.

"Abin bacin rai ganin wannan lokaci mai cike da tausayi Messi na ban kwana da Barcelona, Babu wani ɗan wasa a tarihin wasanni da ya taba sanya kungiyarsa farin ciki kamar Messi, yayi abubuwan da ba za a taba mantawa da su ba, nasarori da dama ga kungiyar," in ji Gary.

Tafiyar Messi ba kawai Barcelona ta taba ba, aa har ma da gasar La Ligar da za ta yi asarar dan wasan da ya fi kowa yawan cin kwallaye a tarihi.