PSG ta fara tattaunawa da Messi

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba Barcelona ta ce Messi mai shekara 34 ba zai ci gaba da murza mata leda ba saboda rashin cimma yarjejeniya

Kungiyar Paris St-Germain ta fara tattaunawa da wakilan Lionel Messi bayan barinsa Barcelona.

An gaya wa BBC cewa tattauna wa tsakanin Messi da PSG da aka yi a ranar Alhamis ta nuna cewa Barcelona ba za ta girmama yarjejeniyar da suka cimma ba.

Za a ci gaba da tattaunawar a ranar Asabar, lokacin da ake tsaka da boye yarjejeniyar da suke yi.

A ranar Alhamis ne Barcelona ta ce Messi ba zai ci gaba da zaman a kungiyar ba.

Sun dora alhakin hakan kan "matsalar kudi da sauya yanayin kungiyar" game da tafiyar dan wasan da ya kwashe shekara 21 a Barcelona.

A ranar Juma'a ne shugaban kungiyar Joan Laporta ya ce idan Messi ya ci gaba da zama a Barcelona hakan zai iya jefa kungiyar cikin babbar matsala ta shekara 50.

Messi mai shekara 34 ya zama ba shi da kulub tun daga ranar 1 ga watan Yuli lokacin da kwantaraginsa ta kare.

Ya kuma yarda cewa zai kara zaman wasu shekaru 5 masu zuwa tare da rage albashin da ake bashi - sai dai kungiyar ba za ta iya ci gaba da rike dan wasan ba.

Idan Messi ya koma PSG zai hadu da abokan wasansa irinsu Di Maria da suke kasa daya, da Neymar da suka buga Barcelona tare da kuma abokin hamayyarsa Sergio Ramos.

Kungiyoyi biyu ne aka fi sa ran za su dauki dan wasan PSG da Manchester City inda tsohon kocin dan wasan Pep Guardiola ya ke.