Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Afirka Ta Kudu: Abubuwan da suka faru a mummunan tashin hankalin da aka shafe mako guda ana yi a Durban
- Marubuci, Daga Andrew Harding
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a birnin Durban, Afirka Ta Kudu
Makonni biyu bayan da kasar Afirka Ta Kudu ta fuskanci kwasar ganima da kuma kone-kone - a tashin hankali mafi muni tun bayan komawa tafarkin dimokaradiyya a shekarar 1994 - an kwashe tulin tarkace da shingayen da aka toshe kan tituna a birnin Durban mai tashar jiragen ruwa.
Amma kuma sojoji na ci gaba da sintiri a unguwannin da tashe-tashen hankulan da aka shafe tsawon mako ana yi suka fi muni, da suka haddasa mutuwar mutane fiye da 300.
"Komai ya tafi. Ba ni da inshora. Na damu matuka game da makomar Afirka Ta Kudu. Na damu matuka game da makomar 'yayana,'' in ji wata 'yar kasuwa Dawn Shabalala, wacce aka wawashe kananan shagunanta hudu - har da su bututun ruwa da kayayyakin hada wutar lantarki.
Ta tuna kallon abubuwan tsoro da haushi a yayin da 'yan sandan yankin suka gaza tabuka komai wajen dakile barnar.
"Ina fargabar zai sake aukuwa. Amma ina zan tafi? Me zan yi? Ina da ma'aikata 12 da ba zan iya biyansu ba. Gwamnati ba ta kula da halin da muke ciki ba," a cewarta, yayin da take tsaye a shagon gyaran gashinta da aka wawushe a kan titin da aka wawushe ko wane shagon da ke wurin, da dama kuma aka kone su kurmus.
Tarzomar da 'aka haddasa'
Bayan fitowarsa daga zaman tattaunawa tsakanin shugabannin larduna da na kasa baki daya game da tashin hankalin, Firimiyan lardin KwaZulu-Natal, Sihle Zikalala, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin "babban bala'i."
A baya Mista Zikalala ya fuskanci suka kan kalamansa na cewa muddin ana son shawo kan tashin hankalin, dole sai mahukunta sun sako tsohon shugaban kasa Jacob Zuma daga gidan yari.
Cafke Zuma da aka yi kan raina umarnin kotu ne ya haddasa barkewar tashe-tashen hankulan, tare da ikirarin cewa aminansa na yunkurin kifar da gwamnatin jaririyar dimokaradiyyar Afirka ta Kudu.
Amma daga bisani Mista Zikalala ya bi bayan gwamnati, inda ya tabbatar da cewa tashin hankalin da ya faru a lardinsa da kuma tsakiyar lardin Gauteng mai masana'antu" ya fara ne saboda tsohon shugaban kasar, amma kuma ya rikide ya zama wani abu da aka gaza shawo kai".
"Da gangan aka fara kuma shirya shi aka yi…. kuma yana da alamun kokarin kifar da gwamnati - yin tawaye ne," Mista Zikalala ya kara fada.
Ko da yake "da dama, mutane da dama ba su ji dadi ba game da daure Zuma ba," Mista Zikalala ya ce, "duk wanda ke da hannu wajen zuga, ko tsarawa ko kuma goyon bayan tashin hankalin, dole a cafke tare da hukunta shi''.
Ya yi kama da fagen yaki
A Phoenix, daya daga cikin unguwannin da suka fi fuskantar tashin hankali mafi muni, al'umma Indiyawa masu yawa mazauna yankin sun nuna damuwarsu cewa wadanda suka shirya tashin hankalin ne suka kuma rura wutar rikicin mai nasaba da kabilanci da gangan, kuma jami'an tsaro suka gaza kare al'umomin.
"Ya zama sai ka ce fagen yaki. Wani abu ne da aka shirya. Abu ne da alamu suka nuna. Wadannan mutane ne da aka horar sosai. Suna kokarin haddasa yakin basasa a wannan kasar. Hari ne na kai tsaye - a kan al'ummar Indiyawa,'' in ji Marvin Govender, daga kungiyar mazauna yankin.
Amma ya yi nuni tare da nuna gamsuwar cewa "daga bisani al'umomin ne suka rika kare kan su."
Akwai kuma zarge-zargen nuna wariyar launin fata, da tsarin kai hare-hare da kashe-kashe ta dabarun nuna ayyukan 'yan banga.
Yayin da yake bayyana damuwa game da lamarin, Ministan 'Yansanda ya Afirka ta Kudu Bheki Cele ya bayar da misalin abinda ya faru na wata mata bakar fata da aka dakatar a wani shingen binciken ababan hawa da ba na hukuma ba.
"Ta shaida min cewa a yayin da aka tsayar da ita kana aka bincika ko ina. Cikin motarta, ana ta barin sauran motocin da Indiyawa ke tukawa suna wucewa ba tare da an dakatar da su ba. An kuma kai ta bakin wani kogi da ke kusa inda aka ci zarafinta, an kuma rika tafka muhawara kan ko dole a kashe ta ko kuma a kyale ta. An kuma kona motar,'' Mista Cele ya ce.
Goyon bayan Zuma
Indiyawa - wadanda suka fara isowa Afirka ta Kudu a cikin karshen karni na 1800 a matsayin leburori haya - su ne kashi 2.6 bisa dari na yawan al'ummar kasar Afirka ta Kudu. Akasarinsu na zaune ne a lardin KwaZulu-Natal.
A unguwar da indiyawa suka fi yawa a garin Verulam, Nasreen Peerbhay ta ce an kashe mijinta Mohammed Rahoff Sathar a wani shingen binciken ababan hawa da ba na hukuma ba da aka kafa a yankin.
Faifen bidiyo daga wurin, a kan babbar hanya kusa da shagon iyalan, yan una wata jar mota gudu kai tsaye cikin taron jama'a.
"Akwai maza bakaken fata biyar a cikin motar. Yana tukawa cikin tsananin gudu inda ya kade mutane takwas, biyar daga cikin sun samu munanan raunuka. Mijina na daya daga cikin wadanda suka mutu. Wani mummunan al'amari ne, kana marar dadi.T An yi sarar rayukan mutane da dama a cikin kwanaki kadan,'' ta ce.
A wata kotu da ke kusa, sojoji da 'yansanda na taimakawa wajen raba taron jama'ar Indiyawa da 'yan Afirka da ke zanga-zanga game da cafke wasu da dama da ake zargi.
Wani ma'aikacin kamfanin gine-gine Thobile Mkhize, na tsaye a cikin taron mutane kadan masu zanga-zangar, sanye da rigar shat mai dauke da hoton Zuma, tare da rera wakokin da suka yi fice a lokacin da ake fafutikar adawa da mulkin nuna wariyar launin fata da aka kawo karshensa a shekarar 1994, bayan kafuwar jam'iyar African National Congress (ANC) - wacce ta kai marigayi Nelson Mandela - kan karagar mulki.
"Ba mu yarda da bangaren shari'a ba," in ji Miss Mkhize, tare da daga murya tana ihu "Zuma!"
Kafin a daure shi, tsohon shugaban kasar ya sha nanata nuna shakku game da dattakun manyan alkalan kasar, tare da zarginsu kan nuna masa banbancin siyasa, da ya sa Kotun Tsarin Mulki ta zargi Zuma kan yunkurin '' yin zagon kasa ga bin doka da oda''.
An dora alhakin faruwar rikicin a kan talauci
Da alamu mutane da dama babban birnin Durban na lardin KwaZulu-Natal - da suka kadu matuka game da girman tashin hankalin - sun amince cewa Zuma da aminansa a cikin jam'iyar ANC mai mulki za su fuskanci martani mai tsauri.
"Sun gaza. Ba zu lalata al'ummominsu ba. Wata hanya ce ta karawa al'ummomin karfin gwuiwa su kara karfi, kana daga duka kasashen daban,'' in ji Anthony Kirkwood, wani daraktan kasuwanci a yankin.
"Ina ga wani abu mafi girma ne da muka shaida."
Amma kuma, wani mai fafutika Nkosentsha Shezi, wanda ke jagorantar sabuwar kungiya mai yi wa gwamnati matsin lamba da ke nuna goyon bayan kiran da Mista Zuma ke yin a ''kawo sauyi ga tattalin arziki'', ya ce babu wata shaida da ta nuna alakar tsohon shugaban kasar da magoya bayansa da tashin hankalin, kana ya ce batu ne na talauci da ya dabaibaye bakaken fatar Afirka ta Kudu wadanda su ne ya fi shafa.
"Mutane a shirye suke su sadaukar da rayuwarsu wajen kare akidar da tsohon shugaban kasa Jacob Zuma ya jajirce a kai. Wannan ba yaki da fararen fata bane. Wannan ba yaki da Indiyawa bane. Batun sake sauya tsarin mulkin nuna wariyar launin fata ne.
"Akasarin bakakane fatar… wadanda suka je rukunan shagunan da sauran wurare suka yi ta kwasar ganima, bas a dauke da mashi, ko bindigogi. Ko shakka babu su ne wadanda yakin ya fi shafa, wadanda aka rika harba da sunan kare dukiyoyin jama'a," in ji Mista Shezi.
Karin labarai kan Afirka Ta Kudu: