Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jacob Zuma: Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu ya soma zaman gidan yari na wata 15
'Yan sandan Afirka Ta Kudu sun tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma na hannunsu.
Mista Zuma ya mika kansa ne bayan mako daya da aka same shi da laifin raina kotu, aka kuma yi masa hukuncin daurin wata 15 a gidan maza.
A daren da ya gabata ne Jacob Zuma ya yarda ya mika kansa ga 'yan sandan da suka iske shi har cikin gidansa suka tattauna domin kawo karshen nokewar da ya yi.
Ya mika kansa ga hukuncin zaman gidan sarka na wata 15, da kotu ta yanke masa ranar 29 ga watan Yuni kan samunsa da laifin raina ta.
Mista Zuma ya ki amsa gayyatar kotun ta bayar da bahasi kan binciken cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa na shekara tara.
Hukuncin kotun ya haifar da wata dambarwa ta shari'a da ba a taba gani ba a kasar ta Afirka Ta Kudu, inda kotun ta sanya wa'adin zuwa karfe 12 na dare agogon kasar (goma na dare na GMT), a kamo shi idan ya ki mika kansa, bayan da ya ki mika kan nasa a ranar Lahadi.
Tsohon shugaban ya tafi wani gidan yari ne da ke kusa da gidansa a lardin KwaZulu-Natal cikin kwambar motocin jami'an tsaro domin fara zaman wannan hukunci.
Tun da farko 'yan sanda sun yi gargadin cewa za su kama Mista Zuma mai shekara 79, muddin ya ki mika kansa zuwa karshen ranar ta Laraba.
A wata 'yar takaitacciyar sanarwa, gidauniyarsa ta ce Shugaba Zuma ya yanke shawarar bin umarnin tsare shi.
Sai kuma daga baya 'yarsa Dudu Zuma-Sambudla ta rubuta sako a shafinta na Twitter cewa mahaifinta na kan hanya ( ba ta rubuta zuwa gidan yari ba), kuma yana cike da karsashi.
Wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban na Afirka Ta Kudu da suka kasa suka tsare a kofar gidansa, da zumar hana kama shi, sun nuna bacin ransu a kan hukuncin da aka yi masa.
Babu wani tsohon shugaban kasar ta Afirka ta kudu da aka taba daurewa kafin wannan lokaci.
Shi dai Mista Zuma har kullum yana bayyana lamarin da cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne ake masa.