Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya yi sulhu da abokin hamayyarsa Gbagbo

Ivory Coast's President Alassane Ouattara shakes hands with former President Laurent Gbagbo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tshohon Shugaba Laurent Gbagbo da Shugaba Alassane Ouattara sun yi sulhu

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara da babban abokin hamayyarsa Laurent Gbagbo sun rungumi juna a haduwarsu ta farko tun bayan yaƙin basasar ƙasar shekaru goma da suka gabata.

Yaƙin ya faru ne bayan da Mista Gbagbo ya ƙi amincewa da kayen da ya sha a zaɓen kuma mutum 3,000 suka rasa rayukansu.

Mista Gbagbo ya koma Ivory Coast a watan jiya bayan da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC ta wanke shi kan tuhume-tuhumen da ake masa na cin zarafin bil Adama.

Mutanen biyu sun jima suna neman shiri da juna.

Mista Ouattara ya yi wa Miista Gbagbo maraba a fadar shugaban ƙasa a Abidjan, babban birnin ƙasar ranar Talata.

"Ina farin ciki da ganinka," shugaban ya ce wa Mista Gbagbo.

Hotuna sun nuna mazan biyu suna murmushi tare da riƙa hannuwa yayin da ake ɗaukarsu hoto.

Mista Ouattara ya ce sun yi sulhu a tsaknainsu kuma sun manta da abin da ya faru.

"Zaman lafiya a ƙasarmu ya fi komai muhimmanci," a cewarsa.

Mista Gbagbo ya yi kira da a saki fursunonin da ake tsare da su tun yaƙin basasar kasar.

Wasu na ganin wannan ganawa a matsayin wata alama ta samar da masalaha a ƙasar amma kakakin Mista Gbagbo Justin Katinan Kone ya bayyana cewa "kada mutane su fiye damuwa da abin da zai faru".

An kama Mista Gbagbo ne a fadar shugaban ƙasa a watan Afrilun 2011 sannan aka kai shi kotun ICC da ke The Hague. Bayan da kotun ta wanke shi neya zauna a Brussels kafin Mista Outtara ya gayyace shi ya dawo ƙasar Ivory Coast.

Mista Gbagbo ya koma a watan jiya kuma magoya bayansa sun yi masa lale.

Har yanzu yana fuskantar ɗaurin shekara 20 bayan da aka yanke masa hukunci da ba ya nan kan laifin satar kuɗin wani bankin yanki lokacin yaƙin basasar.

Kwanan nan ne Mista Gbagbo ya sanar da cewa shi da tsohon shugaba Henri Konan Bedie za su hada kai su yi takara da Shugaba Ouattara.