Afirka Ta Kudu: Abin da ya sa na jefa ƴata ƙasa daga saman bene

Bayanan bidiyo, Matar da ta cillo ɗanta daga saman benen da ya kama da wuta

Wata uwa ta wacce ta jefa jaririyarta cikin taron jama'a, daga saman benen da ya cika da hayaki bayan da aka banka masa wuta a birnin Durban mai tashar jiragen ruwa na Afirka ta Kudu ta shaida wa BBC irin godiyar da ta ke mika wa wadanda suka cece 'yar tata, wacce za ta cika shekaru biyu cikin wata mai zuwa.

"Abinda kawai na iya yi shi ne in amince da mutanen da ban sani ba,'' Neledi Manyoni ta ce. Ta kara da cewa dukansu suna cikin koshin lafiya.

Masu kwasar ganima ne suka bankawa ginin da suke ciki ne wuta.

Tashin hankalin ya barke ne bayan da aka tsare tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a gidan yari.

An sami mai shekaru 76 da aikata laifin raina umarnin kotu a cikin watan da ya gabata, bayan da ya ki halartar gayyatar da aka yi masa kan binciken cin hanci da rashawa a lokacin shugabancinsa.

A ranar Larabar da ta gabata ne ya mika kan sa ga 'yansanda don fara zaman gidan kaso na watanni 15, amma kuma hakan ya haifar da mummunar zanga-zanga, da kone-kone, da kwasar ganima a mahaifarsa da lardin KwaZulu-Natal kuma ta bazu zuwa sauran birane da garuruwa.

Mutane akalla 72 ne suka mutu a irin abinda shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana a matsayin tashin hankali mafi muni a Afirka ta Kudu da aka shaida tun a cikin shekarar 1990, kafin a kawo karshen mulkin fararen fata tsiraru.

Gwamnati ta ce za ta aike da wasu sojoji 25,000 don dakile tashin hankalin.

Ta yaya aka ceci Melokuhle?

Mai daukar hoto na BBC Thuthuka Zondi ya nadi faifen bidiyon Miss Manyoni na jefa Melokuhle, a lokacin suna tsaye a bakin titin tsakiyar birnin Durban a ranar Talata bayan da masu kwasar ganima sukakai farmaki.

Jaririyar lokacin da ake jefo ta ta saman bene
Bayanan hoto, Miss Monyana ta yi kokari ta kutsa ta cikin farfajiyar hawa na biyu na benen inda ta roki masu wucewa da su taimaka mata

Wadanda suka kai samame a kasan benen mai shaguna sun fara banka wa ginin da Miss Manyoni ke ciki wuta, inda ta saba kai wa abokin zaman ta ziyara.

Suna zaune a hawa da 16 na rukunan gidajen a lokacin da suka lura da hayaki na tashi.

Na'urar hawa da sauka ta daina aiki saboda wutar, don haka Miss Manyoni ta ruga da gudu tana sauka ta kan kafar benen tare da jaririyarta.

Amma kuma ta kasa isa kasan benen saboda an riga an toshe.

Ta ce ta yi kokarin kutsawa ta cikin farfajiyar hawa na biyu na benen inda ta roki masu wucewa da su taimaka.

"Abinda na iya tunani shi ne in tabbatar da ganin na ceci rayuwar jaririyata,'' ta ce.

Ma'aikatan kwana-kwana sun isa wurin kusan mintina 20 bayan da mutanen da ke wurin suka fara ceto sauran mazauna cikin ginin ta hanyar amfani da tsani - wanda a lokacin ne Miss Manyoni da sake haduwa da 'yarta.

Ta shaida wa BBC cewa ta yi kokarin dawowa cikin gidan da tsakar dare.

Sarkin Zulu ya yi kira a kwantar da hankali

Kwanakin da aka shafe ana tashin hankalin ya haifar da karancin burodi da man fetur a birnin Durban, inda aka samu dogayen layuka a wajen shaguna da gidajen mai.

A ranar Talata ne matatar mai mafi girma a Afirka ta Kudu ta sanar da cewa ta dakatar da ayyukanta, saboda tashin hankalin da ke faruwa a kasar da toshe hanyoyi rarraba man fetur a ciki da wajen lardin KwaZulu-Natal.

Wani mai kwasar ganima na jan kaya a kasa a wajen rukunan shagunan da aka yi wa karkaf a yankin Vosloorus, da ke wajen birnin Johannesburg,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwasar ganima a shaguna da manyan dakunan ajiyar kaya sun haddasa karancin wasu kayayykin

Haka kuma, babban daraktan kungiyar manoma mafi girma a Afirka ta Kudu AgriSA, ya ce manoman na fama da wahalhalu wajen kokarin kai amfanin gonarsu zuwa kasuwa saboda lalacewar motoci.

"Muna son a dawo da doka da oda ba tare da batalokaci ba, saboda mun shiga cikin mummunan yanayi na tashin hankalin da ya shafi al'umma,'' Christo van der Rheede ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

A kalamansa na farko cikin bainar jama'a, Sarkin Zulu Misuzulu kaZwelithini ya yi tur da masu sace-sacen, yana mai cewa wani bata suna ne ga al'ummar yankin, kana barnar za ta shafi talakawa ne kawai.

"Ban taba tsammanin al'ummar mahaifina za su kasance cikin hali na kona wa da lalata kasarsu ba," ya ce.

"Sanin cewa duk hakan na faruwa a lokacin annobar korona, kana a daidai lokacin bullar sabuwar kwayar cutar mafi hadari, na nuna cewa al'ummar mahaifina na kashe kan su da kan su,'' in ji Sarki Misuzulu, wanda aka nada bayan mutwar iyayensa a baya-bayan nan.