Jacob Zuma: Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu zai sha ɗaurin wata 15

Asalin hoton, AFP
Babbar kotun Afirka Ta Kudu ta yanke hukuncin ɗaurin wata goma sha biyar kan tsohon shugaban kasar Jacob Zuma.
Hakan na faruwa ne bayan Kotun Tsarin Mulki ta kama shi da laifin raina ta bayan ya ki gurfana a gaban kwamitin da ke bincikensa kan cin hanci lokacin da yake shugaban kasa.
Shugabancin Mr Zuma, wanda ya zo karshe a 2018, ya sha fuskantar zarge-zargen cin hanci.
An sha zargin 'yan kasuwa da hada baki da 'yan siyasa wajen juya alakar harkokin gwamnati.
Tsohon shugaban kasar ya gurfana a gaban kwamitin sau daya kacal amma daga nan bai sake zuwa gaban kwamitin ba.
Kwamitin binciken - wanda mai shari'a Raymond Zondo yake jagoranta - ya yi kira ga Kotun Tsarin Mulkin ta tsoma baki.
Babu cikakken bayani kan ko yanzu za a kama Mr Zuma.
A wata shari'ar ta daban, a watan jiya Mr Zuma ya musanta zargin cin hancin da ya kai $5bn (£3bn) kan sayar makamai daga shekarun 1990.











