Ra’ayi a kan samun ‘yancin Sudan Ta Kudu: Matuƙar farin ciki da samu ‘yanci

A crowd gathers during a ceremony in the capital Juba on July 09, 2011 to celebrate South Sudan's independence from Sudan

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Nichola Mandil
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Juba, South Sudan

Bayan fita daga cikin takunkumin gallazawa da nuna wariya da na addini a kasar Sudan, ina zaune a matsayin mai 'yanci kamar ko wane dan kasa a Sudan Ta Kudu tun bayan samun 'yancin kai shekaru goma da suka gabata.

Amma kuma, miliyoyin 'yan kasar ba su samu dama irin wannan ba, saboda suna fama da matsalolin da yakin basasa ya haifar, ya kuma yi nakasu ga 'yancin cin gashin kan namu.

Ya kuma haddasa matsalolin yunwa a fadin kasar, wanda kungiyar bayar da agaji ta Save the Children ke yin gargadi a wata sanarwa da ta fitar wacce ta zo daidai da ranar bikin samun 'yancinmu, cewa mutane sama da miliyan bakwai - fiye da rabin al'ummar kasar - yanzu suna dab da fadawa cikin matsananciyar yunwa ko kuma ma sun riga sun fada cikinta.

A matsayina na Kirista kuma bakar fatar Afirka, ina iya tunawa karara a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 2011 lokacin da kasarmu ta samu 'yanci a matsayin kasa mai cin gashin kanta, bayan shafe shekaru 30 muna gangamin nuna adawa da gallazawa da mamayar Larabawa da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Ko shakka babu na kasance cikin halin bakin ciki saboda mahaifina mai shekaru 85 Dominic Mandil Ukeil ya mutu kuma an binne shi a ranar da muka samu 'yancin kai a mahaifarshi wato Wau, mai nisan kilomita 500 (mil 310) daga Juba babban birnin kasar.

Ni kadai ce a cikin iyalan da suka zabi kaurace wa jana'izar saboda ba kamar sauran ba, ina zaune ne a birnin na Juba, kuma ina son na shaida bikin ranar da aka 'yanta kasarmu.

A lokacin da abokai da makwabta suka zo gidana domin yi min ta'aziyya, na riga na wuce zuwa dandalin samun 'yancin kai.

South Sudanese residents sang and danced during independence celebrations in Juba, South Sudan, Saturday July 9, 2011

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Murna ta cika 'yan kasar Sudan Ta Kudu lokacin da suka samu 'yancin kai

A matsayina na ma'aikaciyar gidan rediyo, na yi la'akari da cewa aikina ne na yada abubuwan da ke faruwa ga miliyoyin 'yan kasar Sudan Ta Kudu da ba su da halin zuwa Juba domin su shaida bikin mai dimbin tarihi.

Ina tsaye a karkashin tutar Sudan Ta Kudu a lokacin da aka kafa ta, kuma aka saukar da ta Sudan kasa saukewar karshe.

Bayan da muka samu 'yancin kai, mun kuma rera taken kasar Sudan rerawa ta karshe, taken kasar wacce ake tilasta wa dalibai - musamman a makaratun kasar da ke Khartoum, babban birnin arewacin kasar - rerawa a ko wace safiya a matsayin "girmamawa ga kasa" da ba mu taba samun kanmu a matsayin 'yayanta ba.

Bikin samun sabuwar kasar tamu ya kunshi rera taken kasar Sudan Ta Kudu, sai kuma gagruman bukukuwa suka biyo baya.

An tsare gwaggona a karkashin dokar Musulunci

Shugaban kasar Sudan na wancan lokacin Omar al-Bashir shi ne babban bako a waccan rana, kuma ganin sa a wurin wani babban abin alfahari ne - tsohon mai gallaza mana - daga karshe yana nuna cewa yanzu mun zama kasa mai cin gashin kanta, mai shugaban kasa bakar fatar Afirka.

Bashir ya zo a wannan rana a matsayin shugaban Hadaddiyar Sudan, kana ya tafi a matsayin shugaban kasar da ta rabu.

Map
1px transparent line

Na jinjina masa kan kasancewa shugaban kasar Sudan wanda ya amince da bukatunmu na samun 'yancin kai, amma iyalaina - kamar sauran mutane - har yanzu suna cike da bakin ciki na salon mulkinsa.

Mulkinsa ya kafa tsauraran dokokin addinin Islama, kana ya rika kokarin musuluntarwa da kuma mayar da mu Larabawa.

Abu mafi muni da bakin ciki da dangina suka gani a shekarar 2004 shi ne, a lokacin da aka yanke wa gwaggo Teresa Farajalla Gindu- lokacin tana da shekaru 65- hukuncin watanni shida a gidan yari a bisa aikata laifin dafa barasa a gidanta da ke birnin Khartoum, wanda ya saba wa dokar addinin Musulunci.

An rufe mini fuska tare da cin zarafina

Kafin mu samu a sako ta, an bukaci mu biyar tarar fam 5,000 na kasar Sudan. Kudi ne masu yawa, kuma ba mu da su. Na yi aiki tukuru, tare da kara yawan sa'o'in aikin domin na samu na biya tarar cikin watanni uku.

Tsare ta da aka yi tsananin mugunta ce, saboda mace ce kuma ba ta da miji, wacce ke sayar da barasa ba wai don tana so ba amma don ta rika samun kudin sayen abinci da sutura ga yara 16 da ke karkashin kulawarta, bayan mutuwar 'yarta da kuma 'yar uwarta, wato mahaifiyata.

A matsayina na babba a cikin yara 16, hakkina ne na kula da su a lokacin da take gidan yari.

South Sudan youths beat drums during celebrations marking three years of independence in Juba on July 9, 2014.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sudan Ta Kudu ce kasa ta karshe da aka kafa a duniya

Bayan shekaru uku a cikin shekarar 2007, an kama ni a birnin Omdurman, a lokacin da nake gudanar da aikin daukar rahoto kan ba-ta-kashi tsakanin dakarun tsaro da kuma tsoffin 'yan tawaye daga birnin Darfur.

Bayan da aka rufe min fuska tare da daure hannayena ta baya, an rika gallaza min a cikin daki mai duhu kuma marar taga da aka tsare ni har na tsawon kwanaki biyar.

Ina da yakinin cewa jami'an tsaron masu nuna wariyar launin fata ne, saboda babu wani dan jarida Balarabe da aka kama sai ni.

A Sudan Ta Kudu, wacce ta samu 'yancin kai, mahukunta sun gayyace ni a shekarar 2014, kuma an yi mini tambayoyi kan dalilan da suka sa na yi hira da manayan 'yan adawa wadanda gwamnati ke fito-na-fito da su.

Kungiyar kare hakkin manema labaraai ta Reporters without Borders ta saka Sudan Ta Kudu a matsayin mai tsanani a fannin 'yancin kafafen yada labarai, inda ta dora ta a kan sikeli na 139 cikin kasashe 180.

Sudan Ta Kudu ba ta gudanar da zabe ba tun bayan samun 'yancin kai, lokacin da Shugaba Salva Kiir ke rike da ragamar mulki.

Karin dama ta samun ilimi

Amma ko shakka babu gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauki tsauraran matakai wajen shawo kan matsalolin kabilanci da nuna wariya da suka rika faruwa a lokacin da muke karkashin mulkin arewaci.

Ana iya ganin sauyi a makarantun gwamnati inda malaman makaranta Musulmai ke koyar da dalibai Musulmai addininsu, kana malaman makaranta Kiristoci na koyar da dalibai Kiristoci darussan addininsu.

Wannan wani gagarumin banbanci ne a tsakanin lokacin mulkin kasar Sudan, lokacin da ake tilasta wa Kiristoci koyon karatun addinin Islama a makarantun gwamnati - sai dai irin wadanda suka taki sa'a kamar ni da na yi karatu a wata makaranta mallakar coci.

Nichola Mandil (C) on 9 July 2011

Asalin hoton, Nichola Mandil

Bayanan hoto, Nichola Mandil (Tsakiya) bai halarci jana'izar mahaifinsa ba domin ya je wajen bikin samun 'yancin kan Sudan Ta Kudu

A karkashin mulkin Khartoum, jami'a daya ce kacal a Sudan ta Kudu har sai a shekarar 1991 ne aka kafa ta biyu. Jami'ar Juba daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1975 har ya zuwa shekarar 2006, na karkashin kasar Sudan.

A yanzu Sudan ta Kudu na da jami'oi 20 - duka a karkashin shugabancin bakaken fata Afirka.

Jami'ar Juba - na da akalla dalibai 10,000 da aka dauka karatu.

Bakaken fata 'yan Afirka - wadanda ke fuskantar nuna wariya a karkashin mulkin Sudan a birnin Darfur, da tsaunakun Blue Nile da Nuba - yanzu suna koyarwa a Sudan ta Kudu.

A watan da ya gabata 'yan Jami'ar ta Darfur suka kammala karatunsu tare da ni - biyu daga cikinsu sun kammala karatun digirinsu na biyu a fannin harkokin hudda da kasashen waje kana na ukun a kan harkokin siyasa. Na kammala karatun digirina na biyu a fannin harkokin hudda da kasashen waje.

Mun gudanar da bukuwan tare, sanin cewa cigaban da muka samu ba zai yiwu ba a Sudan a lokacin mulkin Bashir.

Dubban dalibai daga kasashe - da suka hada da Eritrea, da Ethiopia, da Somalia da kuma Uganda - su ma suna karatu a Sudan ta Kudu.

South Sudanese SPLA soldiers are pictured in Pageri in Eastern Equatoria state on August 20, 2015.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin da aka kwashe shekara da shekaru ana yi wanda ya sa miliyoyin mutane suka rasa muhallansu ya kawo jinkiri wajen samun 'yancin kan Sudan Ta Kudu

Babbar matsalar Sudan ta Kudu ita ce rashin tsayayyen kwanciyar hankali na siyasa, bayan da shugabannin da suka yi fafutikar neman 'yancin kai da kuma mulki, sun jefa kasar cikin yakin basasa da ya haddasa asarar rayukan mutane akalla 400,000, kana fiye da miliyan hudu suka rasa matsugunansu.

Rikicin ya kuma juye zuwa na kabilanci, inda aka kone wasu kauyuka a yankuna masu nisa na Jonglei da Pibor.

Yakin basasar, tare da sauran tashe-tashen hankula na masu nasaba da kabilanci na nufin cewa mutane da dam aba za su iya noma gonakinsu ba, da ya haddasa karancin abincin da ya yi munin gaske.

"Adadin mutanen da ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa ya kai kasha 50 bisa dari idan aka kwatanta da lokaci irin wannna a cikin shekaru goma da suka gabata," in ji kungiyar agaji ta Save the Children a sanarwarta ta baya bayan nan.

Ta kuma kara da cewa mutane kusan miliyan biyu da rabi na cikin "matakin neman agajin gaggawa" kana fiye da 30,000 na cikin mummunan mataki na karancin abinci da matsananciyar yunwa.

"Kungiyar Save the Children na matukar kulawa da jin dadin wasu kananan yara miliyan da kusan rabi da ke fama da matsanancin ciwon tamowa a cikin wannan shekarar, alkaluma mafiya yawa tun bayan shekarar 2013," a cewar sanarwar.

Wannan ya yi mummunan tasiri a kan 'yancin cin gashin kan, amma abin farin ciki shi ne, yanzu Shugaba Salva Kiir da abokin gabarsa Riek Machar sun amince su raba iko a cikin gwamnatin hadin kan kasa, yayin da ake kan tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye a kasar Italiya a karkashin jagorancin Cocin Katolika.

Don haka, a yayin da mu 'yan kasar Sudan da Kudu ke sa rai tare da fatan nan na shekaru goma masu zuwa, za a samu wanzuwar zaman lafiya, yunwa za ta kawo karshe kana dimokaradiyya za ta samu tushen zama don kasarmu ta samu gudanar da zabenta na farko tun bayan samun 'yancin kai.