Shugabannin kasashen turai sun gargadi Iran kan inganta sinadarin uranium

Mutane na wucewa ta kusa da hoton sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi , lokacin zaben da aka yi a watan Yunin 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kasashen turai sun nuna damuwa kan matakin na Iran

Iran ta sanar wa hukumar da ke sa ido kan makaman nukiliya ta duniya cewa ta fara shirin inganta sinadarin uranium.

Iran ta shaida wa hukumar ta IAEA cewa matakin na samar da man fetur ne ga masu bincike. Sai dai ana amfani da sinadarin uranium wajen hada bama-baman nukiliya.

Kasashen turai sun ce matakin na Iran ya keta yarjejeniyar da aka cimma a 2015, kuma babbar barazana ce ga tattaunawar da ake yi. Amurka kuma ta kira hakan mummunan koma-baya.

A yarjejeniyar shekarar wadda aka fi sani da "yarjejeniyar hadin gwiwa", Iran ta amince ta takaita shirin makaman nukiliyarta domin rage hadarin da ke cikin hakan.

Idan ta yi hakan, su kuma manyan kasashen duniya wato China da Faransa da Jamus da Rasha da Amurka da Birtaniya, sun amince su cire mata takunkumin tattalin arziki da suka kakaba mata.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar a shekarar 2018, tare da kara kakaba wa Iran wasu takunkuman. A nata bangaren, Iran ta mayar da martani ta hanyar ci gaba da inganta makamashin nukiliyarta.

Amma lokacin da shugaba Joe Biden ya sha rantsuwar kama aiki, ya sanar da komawar Amurka cikin yarjejeniyar, sai dai Iran na son ya fara janye takunkumin tukunna.

Wakilan Iran da na manyan kasashen biyar na ci gaba da tattaunawa da kokarin ganin an cimma matsaya a taron da za su yi a Vienna, a fakaice kuma wakilin Amurka zai shiga tattaunawar.

An fara tattaunawar ne a watan Afirilu, sai kuma aka sake zama a ranar 20 ga watan Yuni, tare da dagewa zuwa lokacin da har yanzu ba a bayyana ba.

A wata sanarwa da hukumar IAEA ta fitar ta ce: "A yau, Iran ta shaida mana cewa ta soma inganta sinadarin uranium da kashi 20 mai lamba U-235 an kuma tafi da shi cibiyar bincike da ke Esfahan, inda za a sauya shi ya koma sinadarin uranium nau'in tetrafluoride, daga nan kuma a sake mayar da shi wani nau'in na daban kuma daga bisani a yi amfani da shi wajen samar da man fetur."

Sai dai ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da Birtaniya da Faransa sun ce sun damu matuka kan matakin na Iran.

Tattaunawar Vienna

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tattaunawar da za a yi a Vienna, ci gaba ce ta wadda aka dage a ranar 20 ga watan Yuni

Sanarwar da ministocin suka fitar ta hadin gwiwa na cewa: "Iran ba ta da wata hujja da ta shafi farar hula da za ta sanya ta bukatar sinadarin uranium mai sinadarin karfe a ciki, wanda ake amfani da shi wajen kera makaman nukiliya.

Matakin da Iran ta dauka babbar barazana ce ga fatan da ake da shi a tattaunawar da ake yi ta Vienna."

Sanarwar ta kuma bukaci Iran ta koma teburin tattaunawar ta Vienna.

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida a Amurka Ned Price, ya ce duk da cewa ba a sanya ainihin lokacin da za a shiga tattaunawar ba, "matakin inganta sinadarin uranium da Iran ke yi zai iya sauya tunanin da muke yi a kanta".