Wasiƙa daga Afirka: Shekara kusan 30 da kulle iyakar Aljeriya da Morocco duk da kusancinsu

Asalin hoton, AFP
Ciki jerin wasiƙun da 'yan jaridar Afirka ke aiko mana, ɗan jarida ɗan ƙasashen Aljeriya da Canada Maher Mezahi, ya ɗiga ayar tambaya game da dalilin da ya sa aka rufe iyakar Moroko da Algeriya ta kasance a rufe tsawon shekaru.

Ana kiran babbar hanyar shiga Aljeriya daga Moroko Zouj Beghal, ma'ana "Alfadari Biyu".
Wata hikaya ta ruwaito cewa an taɓa tanadar wasu alfadarai biyu a Moroko sannan aka umarce su da nausa wa gabas har sai sun samar da abin da yanzu ake kira iyakar Moroko da Aljeriya.
A wannan yankin namu da ke da iyakoki masu sarari, ban yi mamakin jin wannan tatsuniyar ba.
Iyakar mai faɗin kilomita 2,000 ta kasance wata hanyar jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ƙasashen, ciki har da yaƙin 1963 bayan Moroko ta yi iƙirarin kama wani a Aljeriya.
Alaƙa ta sake taɓarɓarewa lokacin da Aljeriya ta goyi bayan fafutukar Polisario Front da ke neman kafa ƙasar Yammacin Sahara daga Moroko, abin da ya jawo yaƙi daga 1975 zuwa 1991.
Sai aka sake rufe iyakar a 1994 saboda dalilan tsaro, bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani otel a garin Marrakesh na Moroko mai ɗumbin tarihi.

Asalin hoton, Getty Images
Alaƙa tsakanin ƙasashen na Arewacin Afirka na da wuyar sha'ani amma zan bayyana ɓacin raina ne a madadin 'yan wannan ƙarnin game da rufe iyakar.
Tsallakawa a asirce
A matsayina na ɗan Aljeriya wanda ya girma a ƙasar waje, na san cewa bambanci tsakanin al'ummomin biyu ba shi da yawa.
A ƙasar waje, muna sallah a masallaci ɗaya, mu taimaki juna yayin bukukuwa sannan mu fafata a wasannin ƙwallon ƙafa tare.
A ɓangaren al'ada da ɗabi'a da harshe, 'yan yammacin Aljeriya sun fi kama da 'yan Moroko fiye da yadda suke da sauran 'yan Aljeriya a ɗaya ɓangaren.
Sai dai an samu sauyi a wannan karon.
A watan Maris, hukumomin Aljeriya sun faɗa wa wasu manoman dabino na Figuig da ke Moroko cewa daga lokacin ba za su sake noma a yankin El Arja ba da ke cikin ƙasar.

Asalin hoton, AFP
Wasu iyalai a Moroko na iƙirarin cewa suna da takardun mallakar filayen waɗanda kakanninsu suka mallaka a ƙarni na 20 kafin kawo ƙarshen mulkin mallaka.
Duk da haka, Aljeriya na tsaurara bin dokar iyakar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙayyade, tana mai cewa yawan safarar miyagun ƙwayoyi ne ya sa ta kori manoman.
A wajen da yawa daga cikin mazauna Figuig, noma ne, hanyar cin abincinsu kuma rufe iyakar na nufin halaka tattalin arzikinsu.

Asalin hoton, AFP
Rikicin na zuwa ne bayan an gabatar da wani ƙudiri na neman a halasta amfani da tabar wiwi don aikin lafiya da kuma kamfanoni.
Daga nan kuma sai hukumomin Aljeriya suka ce ana yin safarar miyagun ƙwayoyi a kan iyakar.
A watan Yuni Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya kawar da yiwuwar buɗe iyakar, yana cewa: "Ba za mu buɗe iyaka da ƙasar da ke sukarmu kusan kullum ba."
Bai yi wani ƙarin bayani ba, amma gwamnatocin kan kai wa juna hari a kafafen yaɗa labaransu.

Asalin hoton, Maher Mezahi
Bayan barci ya kwashe ni a ɓangaren ciyayi da ke gaɓar Tekun Bahar Rum, sai na farka a tsakiyar Sahara da safe a kusa da mashigar Figuig-Beni Ounif.
Na ji daɗin hangen Moroko mitoci daga nesa da kuma ganin jami'an tsaro masu tsaron iyaka.
Matasa tsarana ba su taɓa jin irin wannan daɗin ba kuma da yawa na fatan za a buɗe ta wata rana.


A bayyane take cewa gwamnatocin biyu ba sa son tattaunawa ko cimma matsaya ko kuma ma mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.
Rufe iyakokin na nufin haifar da rashi a tsakanin ƙasashen ƙungiyar haɗin kan Larabawan Afirka ta Arab Maghreb Union.
Ƙasashen ƙungiyar da suka haɗa da Mauritania da Moroko da Aljeriya da Tunisia da kuma Libya, za su iya zama masu ƙarfin faɗa-a-ji a yankin da sun haɗa kansu.












