Yadda matsalar ci-rani ke janyo mace-macen aure a Nijar

GG

Al'adar zuwa ci rani ta yi fice a Jamhuriyar Nijar inda maza matasa ke zuwa wasu ƙasashen Afirka da ma Turai domin rufawa kai asiri.

Jihar Taoua na daya daga cibiyoyin wannan batu na ci-rani a Jamhuriyar Nijar din sai dai al'amarin na haifar da matsaloli a zamantakewar ma'aurata.

Daya daga cikin matsalolin da ci-ranin ke haifarwa shi ne jefa matan aure ga kusanta da mazajen da ba nasu ba, lamarin da ke lalata auratayya.

Sai dai kuma masu ruwa da tsaki na bijiro da hanyoyin magance matsalolin kauce hanya da wasu mata da kuma maza ke yi sanadin ci-ranin.

Wani ɗan garin Kwallema Babba a Taoua, Sahibu ya shaida wa BBC cewa daga cikin dokokin da aka gindaya akwai rage sadakin auren zawarawa da kuma matan da ba su taba aure ba.

Ya ce an samu ci gaba wajen raguwar zawarawa da lalata a yankin sai dai kuma ta wata fuskar, an samu karuwar mace-macen aure saboda ci-ranin.

Wakilin Hakimin Kwallema Babba Alhassan Hamza daya daga cikin wadanda suka tsara dokokin ya bayyana dalilan da suka sa aka yi dokar.

"Iyaye da mutanen gari sun kawo mana shawarar a fito da wani abu da zai takawa matsalar burki". in ji shi.

Ya ce matan da suka kauce hanyar na tsintar kansu cikin tsangwama har ma rasa aurensu.

Abin da dokar ta ƙunsa

A cewar Wakilin Hakimin Kwallema Babba, dokar ta tanadi tarar CFA 500 ga mutumin da ya yi wa matar aure ciki musamman wadda minjinta ya bar ta saboda ci-rani.

"Ita ma matar saboda jan kunne tana biyan tarar CFA 200". in ji Alhassan Hamza.

Ya bayyana cewa a yanzu, suna kokarin fito da tsarin ladabtar da mazajen da ke barin matansu tsawon lokaci da sunan ci-rani.

"Lokacin da aka fara, ba a yi tunanin matsalolin da ka iya faruwa ba, yanzu mun gano cewa shi ma mijin da ya barta yana da laifi" kamar yadda wakilin Hakimin Kwallema Babba ya fada.

Ya ce kudaden tarar da ake karba, ana bai wa miji ne ya je ya yi wani auren. Ya kara cewa ya zuwa yanzu, sun hukunta mutum uku da aka samu da laifin keta dokar.