Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kisan George Floyd: An yanke wa Derek Chauvin hukuncin fiye da shekara 22
An yanke wa tsohon jami'in ɗan sandan Amurka farar fata da aka samu da laifin kisan baƙin Ba-Amurken nan George Floyd a Minneapolis hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara 22 da wata shida a kurkuku.
Alƙalin ya ce an yanke wa Derek Chauvin hukuncin ne la'akari da yadda ya yi amfani da matsayinsa ta hanyar da bata dace ba sannan da irin muguntar da ya nuna ga Mista Floyd.
Mista Floyd mai shekara 48 ya mutu bayan da Chauvin ya danne masa wuya tsawon mintuna tara da rabi.
Mutuwar Floyd ta janyo gagarumar zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata da kuma cin zalin ƴan sanda.
An samu Chauvin, mai shekara 45 da laifin kisa da wasu tuhume-tuhumen da aka yi masa a watan da ya gabata. Lokacin sauraron shari'ar, lauyansa ya bayyana kisan a matsayin "kuskuren da aka yi da kyakkyawar niyya".
An kuma buƙaci Chauvin ya yi rajista a matsayin mai laifi sannan an haramta masa mallakar makami tsawon rayuwarsa.
Shi da wasu abokan aikinsa uku duka an tuhume su da take haƙƙoƙin George Floyd.
Iyalan Floyd da magoya bayansu sun yi maraba da hukuncin kotun.
"Wannan hukuncin mai cike da ɗumbin tarihi ya kusanto da iyalan Floyd da ƙasarmu kusa da samun waraka da kuma bin diddigin lamarin," kamar yadda Lauya Ben Crump ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
Ƴar uwar Mista Floyd Bridgett Floyd ta ce hukuncin "ya nuna cewa an fara ɗaukar batutuwan cin zalin ƴan sanda da mahimmanci" amma har yanzu "akwai sauran jan aiki a gaba".
Shugaba Joe Biden ya ce da alama hukuncin ya dace sai dai ya bayyana cewa bai san cikakken bayani kan lamarin ba.
Me aka ce a lokacin yanke hukuncin?
Yayin zaman yanke hukuncin, ɗan uwan Floyd Terrence Floyd ya buƙaci a yanke wa Chauvin hukuncin aƙalla shekara 40.
"Saboda me? Me kake tunani? Me yake yawo a kanka har ka dasa gwiwoyinka a kan wuyan dan uwana?" a cewarsa.
Ƴar Mista Floyd Gianna, mai shekara bakwai ta bayyana cikin wani hoton bidiyo tana faɗin ta yi kewarsa kuma tana ƙaunarsa.
"Ina yawan tambayarsa," a cewarsa. "Babana yana taimaka min wajen wanke bakina."
Alƙalin Peter Cahill ya ce kisan ya sosawa jama'a rai da ƙasar musamman iyalan Mista Floyd.
Chauvin ya faɗawa kotun yana miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan Mista Floyd inda ya ce za a iya samun wasu bayanai a gaba kuma yana fatan abubuwan za su kwantar muku da hankali".
Amma kuma bai nemi afuwa ba.
A kotun, mahaifiyar Chauvin, Carolyn Pawlenty ta ce "danta mutum ne na gari".
Hukuncin da aka yanke wa Chauvin shi ne mafi daɗewa da aka taɓa yankewa wani tsohon jami'in ɗan sanda bisa amfani da ƙarfi har ta kai ga kisa in ji Babban Atoni na Minnesota, Keith Ellison.