INEC za ta ci gaba da bayar da rijistar masu zabe

Asalin hoton, Getty Images
A farkon makon gobe ne, ake sa ran hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijeriya INEC za ta ci gaba da aikin ba da rijistar masu zaɓe a faɗin ƙasar a shirin tunkarar zaɓen 2023.
INEC ta ce a wannan karo, waɗanda suka cancanci yin rijistar za su fara shigar da bayanansu ne ta intanet kafin daga bisani su ke ƙafa-da-ƙafa su kammala a cibiyoyin rijistar da za a samar.
Hukumar zaɓen wadda nan gaba a yau ne za ta ƙarƙare shirye-shiryen aikin rijistar, ta ce burinta shi ne yi wa 'yan Nijeriya miliyan 20 rijista kafin zaɓen ƙasar mai zuwa.
Daraktan hulɗa da jama'a na hukumar, Mista Nick Dazan ya shaidawa BBC cewa bayan tuntuba da suka yi da masu ruwa da tsaki a makon da ya wuce,wato shugabannin jam'iyyu 18, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, da 'yan jarida da shugabannin jami'an tsaro.
''Insha Allahu ranar 22 ga watan nan kwamishinoni na tarayya za su yi nazari akan tuntubar da muka yi, sannan su fitar da jadawalin yadda na yadda wannan rijista za ta kasance.Amma tabbas kamar yadda mukai bayani tun da farko, za a fara yin wannan rijista ranar Litinin 28ga watan Yuni 2021.
Kuma wadanda suka cancanci yin rijistar sun hada da wadanda a baya ba su taba yin rijistar zabe ba, da kuma shekarunsu ya kai 18, da wadanda suke son sabunta rijistarsu musamman wadanda katinsu ya ke da matsala ko dai zanen rubutu ya goge da wadanda aka samu kuskure wajen rubuta sunansu, da wadanda sukai kaura daga wata jiha zuwa wata da sauransu.,'' inji Mista Nick.
Mista Nick ya kara da cewa, a wannan karon ma za a yi rijistar ne ta internet, wanda akwai manhaja ta musamman da za a shiga si a sanya bayanan mutum, wato suna da unguwarka da kuma shekaru da sauransu.
Bayan an gama da wannan fannin, mutum zai garzaya cibiyoyin hukumar zabe domin a dauki hoton ka da zanen yatsu. daga nan za a bai wa mutum katin wucin gadi kamar yadda ake yi a baya. Amma daga baya idan an gama tantancewa za abai wa mutum kati na dindindin da za a yi amfani da shi a lokacin zabe.
Sai dai Mista Nick ya ce yankunan karkara ma ba a barsu a baya ba, sanin cewa babu internet a wuraren, ''daman makasudin amfani da internet shi ne a rage cinkoso a cibiyoyin hukumar zabe kamar yadda aka samu a baya, don haka su tsohuwar hanyar rijista za a bi wajen yi musu.''
Hukumar zaben INEC ta ce kawo yanzu an yi wa kimanin mutum miliyan 84, ana kuma sa ran za a yi wa mutum miliyan 100 nan ba da jimawa ba. Za dai a dauki shekara daya ana gudanar da wannan aiki na yi wa 'yan Najeriya rijistar zabe.











