Ahmed Gulak: Ƴan bindiga sun kashe tsohon mai bai wa Goodluck Jonathan shawara kan siyasa a Imo

Asalin hoton, OTHER
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kashe maharan da suka kashe mai bai wa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha'anin siyasa, Barista Ahmed Gulak.
DSP Bala Elkana, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya shaida wa BBC cewa jami'ansu sun kashe ƴan bindiga 10, kuma sun yi nasarar kwace makamai da motoci daga hannun 'yan bindigan.
"Mun kashe su gaba ɗaya duk matattu ne," in ji shi.
Ya ce maharan sun tare motocin da ke dakon albasa suna ta raba wa mutanensu kuma an yi amfani da motoci aka gano su.
A ranar Lahadi ne ƴan bindiga suka kashe Barista Ahmed Gulak bayan buɗe wa motarsa wuta akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a Owerri.
Rundunar ƴan sandan Imo ta ce lamarin ya faru ne a kusa da yankin Umueze Obiangwu da ke karamar hukumar Ngor-Okpala da ke dab da filin jirgin sama Owerri, babban birnin jihar.
Sanarwar da ƴan sandan suka fitar ranar Lahadi ta ce: "Ahmed Gulak ya bar dakin otal dinsa na Protea ba tare da sanar da 'yan sanda ko sauran jami'an tsaro ba bisa la'akari da halin rashin tsaron da ake fama da shi a yankin Kudu maso Gabas da kuma musamman jihar Imo.
Ya bar otal din ba tare da wani jami'in tsaro yana yi masa rakiya ba kuma motar da ya shiga ta bi wata hanya da ba a saba bin ta ba zuwa filin jirgi, inda 'yan bindiga shida suka tare su suka harbe Ahmed Gulak," a cewar kakakin ƴan sandan Mr Elkana.
A cewarsa, Kwamishinan 'yan sandan jihar Imo Abutu Yaro ya yi umarni a gudanar da bincike kan lamarin.
Gulak ya taɓa rike shugabancin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya kafin ya koma jam'iyyar APC mai mulki.
Kuma ya taɓa zama shugaban majalisar jihar Adamawa.
Buhari ya 'kadu' da kisan gillar da aka yi masa
A sakon da ya aike game da kisan da aka yi wa Ahmed Gulak, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa kan abin da ya kira "mummunan kisan da wadanda ba a san ko su wane ne ba suka yi wa dan siyasar Adamawa Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo State by yet to be identified gunmen."
Sanarwar da kakakin shugaban kasar Malam Garba Sehu ya fitar ta ambato Shugaba Buhari yana cewa: "Na yi matukar damuwa kan irin wannan kisa da wasu shaiduna da suka sha alwashin hana zaman lafiya da hadin kan kasa suka kitsa kan Gulak.""Bari na yi gargadi cewa babu wani mutum ko rukunin mutane da zai yi irin wannan danyen aiki sannan ya yi tsammanin zai sha. Za mu dauki dukkan matakan da ke hannunmu domin mu tabbatar cewa wadannan miyagun mutane sun fuskanci hukunci," a cewar Shugaba Buhari.
Ya jajanta wa iyalan Ahmed Gulak da 'yan uwansa da al'ummar jihar Adamawa da ma dukkan 'yan Najeriya bisa rashin da aka yi.
Jihar Imo na cikin jihohin yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke fama da rikice-rikicen 'yan bindigar kungiyar IPOB da ke son ballewa daga kasar domin kafa kasar Biafra.
Jami'an tsaro na zargin 'yan IPOB da kai hari kan ofisoshin 'yan sanda da na hukumar gyaran hali tare da kashe jami'ansu a jihar ta Imo.











