An saki sauran ɗaliban kwalejin gandun daji da aka sace a Kaduna

Kwalejin Gandun Daji Kaduna

An saki sauran ɗaliban da aka sace na kwalejin Horar da Harkokin Noma da Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya da ke Kaduna.

Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban ya tabbatar wa BBC cewa an saki ɗalibai 27.

Ya ce suna kan hanyar karɓar ɗaliban.

Shiekh Ahmad Abubakar babbam malamin addinin Islama da ke da'awar yin sulhu da ƴan bindiga ya shaida wa BBC cewa su shiga tsakani da aka saki ɗaliban.

"Mu muka yi ƙoƙarin ganin an sake su tare da taimakon tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo," in ji Sheikh Gumi.

Sai dai malamin bai bayyana cewa ko an biya kuɗin fansa ba kafin aka saki ɗaliban.

Gwamnatin jihar Kaduna ba ta tabbatar da sakin ɗaliban ba kawo yanzu.

A watan Maris ne ƴan bindiga suka abka kwalejin gandun dajin da ke unguwar Mando a Kaduna suka saci ɗalibai 30.

Ɗaliban kwalejin Gandun Daji sun shafe kusan wata biyu hannun ƴan bindiga. Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sha nanata cewa ba zai sulhu da ƴan bindiga ko ya biyan kuɗin fansa ba.

Sakinsu na zuwa bayan Iyayen ɗaliban kwalejin na gandun daji a Kaduna sun gudanar da zanga-zanga a harabar ginin majalisa a Abuja a ranar Talata.

Ɗalibai 39 aka sace amma an saki 10 daga cikinsu.