Laurent Gbagbo: Kotun Duniya ta tabbatar da wanke tsohon shugaban Ivory Coast daga laifin keta hakkin dan adam

Asalin hoton, Getty Images
Kotun Hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta tabbatar da wanke tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo daga laifukan keta hakkin dan adam.
Hakan zai ba shi damar komawa Ivory Coast, inda yake da matukar karfin fada aji.
An tuhume shi da hannu a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar Ivory Coast a 2010 mai cike da takaddama wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 3,000.
Shi ne shugaban kasar na farko da aka yi wa shari'a a kotun ICC,kodayake ya sha musanta hannu a rikicin da aka yi a kasar.

Asalin hoton, AFP
Wakiliyar BBC a kotun da ke Hague, Anna Holligan, ta ce ana kallon wannan shari'a a matsayin wani zakaran gwajin dafi ga kotun wajen iya tafiyar da manyan shari'o'i.
Wanne martani aka yi game da hukuncin?
Mr Gbagbo, mai shekara 75, ya jinjina wa kotun ta ICC da ke Hague bayan yanke hukuncin, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Masu goyon bayansa sun taru a wajen kotun suna ta murna.
- Kungiyoyin farar hula na son gwamnatin Nijar ta kori ministan tsaro
- Nijar ta sha gaban ƙasashen Afirka 10 a ɓunƙasar tattalin arziki
- Ali Nuhu ya yi amai ya lashe kan zanga-zangar #SecureNorthA kasar Ivory Coast an yi ta rawa da waka a yankunan da ke goyon bayan Gbagbo da ke wajen birnin Abidjan.
Wani magoyin bayan tsohon shugaban kasar Jean Gossé ya shaida wa AFP cewa "Muna cewa yanzun nan aka 'yantar da daukacin Afirka.... Shi ya sa muke ta murna. Wannan rana ba za a taba mantawa da ita ba a tarihinmu."
Tsohon shugaban kasar ya je kotun tare da amininsa kuma tsohon shugaban matasa Charles Ble Goude, wanda aka zarga da jagorantar kungiyoyin da ke goyon bayansa.
An wanke dukkan mutanen biyu daga laifi a 2019, sai dai masu shigar da kara sun daukaka kara bisa abin da ake ganin mataki ne da ya ba su mamaki.
Tsohon shugaban na Ivory Coast yana zaune ne a Brussels tun da aka sake shi daga gidan yari shekaru biyu da suka wuce.
Mutumin da ya gaje shi kuma tsohon abokin hamayyarsa, Shugaba Alassane Ouattara, ya gayyace shi ya koma Ivory Coast, kasar da ke fafutukar ganin an samu zaman lafiya.

Asalin hoton, AFP/EPA
A shekarar da ta gabata an samu mummunan tashin hankali, lokacin da babban abokin hamayyar Mista Gbagbo, Alassane Ouattara ya sanar da aniyarsa ta neman tazarce a wa'adi na uku a kujerar shugabancin kasar ta Ivory coast.
Rikicin bayan zaben na 2010 ya tashi ne lokacin da Laurent Gbagbo, wanda ya kasance a kan mulki tsawon shekara goma, ya ki yarda da shan kaye a hannun Ouattara.











