An sako fasinjojin NSTA da aka yi garkuwa da su a jihar Neja

Lokacin karatu: Minti 1

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon sako fasinjojin:

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da sako fasinjojin NSTA da aka yi garkuwa da su a makon da ya gabata.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce ya tarbi fasinjojin guda 53 a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya wallafa hotuna da bidiyon fasinjojin lokacin da suke shiga gidan gwamnatin da kuma lokacin da suke zaune.

Sai dai babu ƙarin bayani kawo yanzu kan yadda mutanen suka samu ƴanci.

An sace fasinjojin 18 ranar 14 ga watan Fabrairu a kusa da garin Zungeru a jihar ta Neja, abin da ke nufin ba fasinjojin kaɗai aka saki ba.

An tare su ne lokacin da suke kan hanyar zuwa Minna daga Kontagora.

Sakin mutanen ya zo ne a dai-dai lokacin da ake jimamin sace ɗaliban makarantar sakandaren Kagara ake kuma fafutukar ganin an kuɓutar da su.

A makon jiya ne wani bidiyo ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna fasinjojin suna roƙon a kai musu ɗauki ta hanyar biya musu kuɗin fansa da ya kai naira miliyan ɗari.

A bidiyon an ga wasu mutane ɗauke da manya-manyan bindigogi suna harbi a iska suna furta wasu kalamai.