Majalisar Amurka ta gaza kama Trump da laifi

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce wanke Donald Trump da majalisa ta yi daga zargin haddasa rikicin matasa a zauren majalisar manuniya ce cewa "dimokuraɗiyya na cikin wani hali".

'Yan majalisar jam'iyyar Republican bakwai ne suka goyi bayan hukunta Trump, abin da ya sa aka kasa samun biyu cikin uku na adadin da ake buƙata domin kama tsohon shugaban da laifi.

Mista Biden ya ce "akwai hujja" kan tuhumar da ake yi wa Trump kan rikicin 'yan dabar da suka kai hari kan ginin majalisar a watan Janairu, yayin da ya buƙaci a jingine batun.

Da rinjayen kuri'u 57 suka kada kuri'ar, inda 43 cikinsu suka ki amincewa - cikinsu har da 'yan Republican bakwai d su ka bi sahu takwarorinsu na Democrat - amma ba su sami kuri'u 65 da suke bukata ba.

Bayan da aka wanke shi daga zargin aikata laifi, Mista Trump ya fitar da wata sanarwa da ke sukar shari'ar, yana cewa "yunkurin neman bata suna ne mafi girma a duniya".

Wannan ne karo na biyu da aka tsige Mista Trump daga mukamin shugaban kasa.

Da a ce an same shi da laifi, da majalisar ta hana shi sake tsaya wa takara sannan ba zai samu wasu alfarma da ake yi tsoffin shugabannin kasar ba.

Bayan an kada kuri'ar, shugaban sanatocin jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawa, Sanata Mitch McConnell ya ce Mr Trump ne yake da "alhakin" yamutsin da aka yi a ginin majalisar dokokin kasar sannan ya bayyana hakan a matsayin "abin kunya da rashin yin aikin da aka dora masa".

Tun da farko, ya kada kuri'ar kin goyon bayan tuhumar Mr Trump, yana mai cewa hakan ya keta kundin tsarin mulki ganin cewa yanzu Mr Trump ba shi ne shugaban kasa ba. Mr McConnell shi ne ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin ba a soma shari'ar Mr Trump ba kafin ya sauka daga mulki ranar 20 ga watan Janairu.

Sai dai Mr McConnell ya ce duk da hakan ana iya gurfanar da Mr Trump a gaban kotu.