Bola Tinubu: Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a jam'iyyar APC kan zaɓen 2023

Asalin hoton, @APCNIGERIA
Wani sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigonta Bola Ahmed Tinubu.
Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ce aikin sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar da ke gudana yanzu haka a jihohin ƙasar baki ɗaya ba shi da wani tasiri.
"Sabunta rijistar da jam'iyyar ke yi tamkar a sanya ɗaya ne kana kuma a cire ɗaya, don haka ni ina ganin ba wata ƙaruwa ba ce'', a cewar Tinubu.
Wannan kalamin ya sa wasu ƴaƴan jam'iyyar na cewa da walakin goro a miya, kuma alama ce da ke nuna cewa bai ji daɗin abin da ake yi ba, saboda a cewarsu, aikin rijistar zai iya rage masa ƙarfin mamayar da ya yi wa jam'iyyar, da kuma tasirin da yake da shi a cikinta.
Alhaji Maikano Zara, ɗan jam'iyyar ne mai rin wannan ra'ayin, da ya ce ''Ba zn goyi bayan sabunta rijistar ƴan jam'iyyar ba ne saboda ya ga cewa buƙatunsa ba su biya ba, ya fi son a tsaya daga ƙauri sai gwiwa''
Sai dai wasu makusantan Bola Tinubun na cewa ba a fahimce shi ba ne, kuma babu yadda sabuwar rijistar za ta shafi ƙarfin fada ajin da yake da shi a jam'iyyar.
Alhaji Ibrahim Masari, jigo ne a jam'iyyar ta APC a Najeriya, wanda ya ce ''Abin da yake magana shi ne da an inganta katin da ake da shi na baya wanda aka samar ta Internet, sai a ɗora a kai ba wai a sake yin wani ba''.
"Sake rijistar jam'iyya ba zai canja komai ba, sannan ba zai rage tasirin mai tasiri ba in har yana da tasirin'', a cewar Masari.

Asalin hoton, Google
Sai dai masana, irin su Malam Kabiru Sufi na kwalejin share fagen shiga jami'a ta jihar Kano na cewa fitar irin wɗannan kalamai daga bakin Bola Tinubu a matsayinsa na jagora, duk kuwa da cewa yana da damar yi wa jam'iyyar gyara tun a matakin shirin rijistar, na nuna cewa akwai ɓaraka.
Har zuwa yanzu dai Mista Tinubu bai fito ya ce yana neman shugabancin Najeriya ba, amma tuni wasu masoyansa suka fara tallata shi.
Ko da yake wasu ruwayoyin na nuna cewa wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC daga arewacin Najeriya ba sa goyon bayan haka.
Majiyoyi sun ce sun fi goyon bayan jam'iyyar ta tsayar da ɗan takara daga shiyyar kudu maso-kudancin ƙasar, lamarin da ya haddasa ka-ce-na-ce.
Wasu ma na cewa akwai tsohon alƙawarin da ƙusoshin jam'iyyar suka kulla cewa shiyyar kudu maso yammacin kasar ce za ta fitar da dan takarar shugaban kasa, a zaben 2023.
Sai dai shugabannin jam'iyyar sun ce har yanzu ba su fara maganar takara ba ballantana karɓa-karɓa.
Ƙarin wasu labarai masu alaƙa











