Rikicin APC: Abubuwan da gwamnonin jam'iyyar suka tattauna da Buhari

APC

Asalin hoton, Twitter/@bashirahmad

Lokacin karatu: Minti 2

Fadar shugaban Najeriya ta yi ƙarin haske game da taron da wasu gwamnonin jam'iyyar APC yi da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talata.

An gudanar da taro ne ta shafin intanet inda aka tattauna kan batutuwa daban-daban, kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasar a shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce gwamnonin sun kai ziyarar ce domin yabawa shugaban kan yadda ya sa baki a rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar, wanda suka ce matakin da ya ɗauka ya janyo an fara samun maslaha kan matsalolin cikin gida na jam'iyyar ta APC.

Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa a ziyarar gwamnonin, an tattauna batutuwan da suka shafi tsaro baya ga na rikicin jam'iyyar.

Tsaro

Game da batun tsaro, Garba Shehu ya ce an samu ci gaba sosai a fannin tsaro saboda "duk wanda ya san inda aka fito zuwa yanzu, ya san an samu gagarumar nasara a kan matsalar rashin tsaro,"

"Shi yankin Kudancin Kaduna ai abin da ake ta jaddawa shi ne yau duk hukuma duk ƙarfinta duk so da take ta kawo zaman lafiya, al'umma da suke zaune a wurin suma su zamana suna shirin zaman lafiya," in ji sa.

A cewarsa, ba a Kudancin Kaduna kaɗai aka samu nasara ba, a Borno da Yobe ma "abubuwa sun yi sauƙi sosai."

Da yake magana kan matsalar tsaro a Katsina da Zamfara, Garba Shehu ya ce "muna tafe, nan ɗin ma za a ga tatas an gama da shi" tun da a baya matsalar tsaron a cewarsa ta fi ta'azzara a Borno da kuma Yobe.

Ya ce rikici musamman tsakanin makiyaya da manoma ya yi sauƙi a Benue da Nassarawa da Plateau da kuma Adamawa.

Wannan layi ne

Tattalin Arzikin Ƙasa

A cewar Garba Shehu, farfaɗowar tattalin arziki abu ne da ba zai faru ba a lokaci ɗaya inda ya ce "abu ne da ba za a tashi yau a ce an wayi gari duk wanda ba shi da komai ya tashi aljihunsa cike da kuɗi ya warware ba."

Ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne irin matakan da gwamnati take ɗauka don ganin cewa ta tada komaɗar tattalin arzikin ƙasar.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya zaɓi noma, ya zaɓi harkar haƙo ma'adinai wanda jama'a miliyoyi suke ta shiga yanzu suna ta yi,"

"Wadanda suka rungumi harkar noma yanzu a Najeriya ba wanda yake da-na-sani musamman harkar shinkafar nan, yanzu an shiga alkama, auduga, an shiga man kwakwa,"

"Haka da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ake ta bi ana ta tura kuɗi da bashi mai sauƙi ga waɗanda suke son su yi waɗan nan sana'oi kuma ana ganin suna samun ci gaba a rayuwarsu." kamar yadda mai magana da yawun shugaban Najeriyar ya bayyana.

Sai dai Garba Shehu ya yi watsi da zargin cewa 'yan siyasa na kashe mu raba da basukan da gwamnati ke bayarwa inda ya ce "suma 'yan siyasa ai 'yan Najeriya ne, amma abin ya fi ƙarfin 'yan siyasa nawa suke a cikin wannan al'uma ta mu,"

"Ana maganar cewa kamar manoman shinkafa sababbi wajen miliyan 12 suka shiga cikin wannan harka."

Wannan layi ne