Wasu 'yan Najeriya na sukar Buhari kan karɓar tubabbun 'yan Boko Haram

Asalin hoton, Others
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
- Lokacin karatu: Minti 3
Da alama wasu 'yan Najeriya ba su aminta da yunƙurin gwamnati ba na sauya tunanin 'yan ƙungiyar Boko Haram tare da mayar da su cikin al'umma duk da cewa ba yanzu aka fara shirin ba.
Sai dai babu mamaki wannan ya fi jan hankali ne saboda ya zo a lokacin da tashe-tashen hankali ke ƙaruwa a ƙasar, musamman a arewacin ƙasar.
A ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli ne Manjo Janar John Enenche, babban jami'in yaɗa labarai na hedikwatar tsaro ta Najeriya ya bayar da sanarwar cewa gwamnati na shirin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 603 bayan ta gama ba su horon sauya musu tunani.
Janar ɗin ya bayyana haka ne yayin da yake yin ƙarin bayani game da ayyukan rundunar na sauya tunanintubabbun 'yan Boko Haram a Abuja, babban birnin ƙasar.
Rundunar na gudanar da shirin mai laƙabin Deradicalisation, Rehabilitation and Reintegration (DRR), wanda aka ƙaddamar tun 2016 ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, ya nuna Janar Abdulmalik Biu, jagoran Bataliya ta 7, yana cewa: "Ɗan Boko Haram ɗin da ya tuba zai iya zama shugaban ƙasa."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
An ga Sanata Ali Ndume - shugaban kwamitin sojojin ƙasa a Majalisar Dattawa - a wani bidiyo yana yin Allah-wadai da shirin.
"Wannan ba abin da za a amince da shi ba ne, ka ajiye mutane a sansani kuma ka ba su kuɗi; kenan ma kana cewa mutane su shiga Boko Haram sannan su tuba domin su zama wasu," in ji shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Me ya fusata 'yan Najeriyar yanzu?
A ranakun ƙarshen mako ne wasu hotuna suka ɓulla ɗauke da wasu mutane sanye da fararen kaya da korayen huluna - tutar Najeriya - cikin wasu tantuna a zaune, waɗanda aka ce 'yan Boko Haram ne da aka gyara wa hali.
Hotunan da suka karaɗe shafukan sada zumunta, sun jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke nuna cewa gwamnati ta fi ji da 'yan Boko Haram sama da waɗanda ƙungiyar ta lahanta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Fatima Adu (@NaijaGoBeta1) ta ce: "Najeriya ta saba saka wa 'yan ta'adda da lada amma ta ƙyale waɗanda suka ('yan ta'adda) lahanta."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Wani mai suna @AyanfeOfGod ya ce: "An yaye 'yan Boko haram 601, a gefe guda waɗanda suka mayar marayu na sansanonin 'yan gudun hijira. Najeriya ta gaza."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
'Yan Boko Haram ma 'yan Najeriya ne - Fadar Gwamnati
Da yake mayar da martani kan zarge-zargen, mai magana da yawun Fadar Shugaban Najeriya garba Shehu, ya ce "bai kamata a nuna musu wariya ba domin su ma 'yan Najeriya ne".
"Idan muka ƙyale su suka koma daji, suka ci gaba da yaƙarmu ai ba a yi dabara ba," in ji shi.
"Idan aka nuna musu wariya ai ba a yi wa ƙasar ma kanta adalci ba."