Muhammadu Buhari: Abubuwa biyar da shugaban Najeriya ya fada a ziyararsa ta Daura

Asalin hoton, Facebook/Femi Adesina
A ranar Asabar ne shugaban Najeriya ya sabunta rijistar zama dan jam'iyyar APC da ke mulkin kasar.
Ya sabunta rijistar ne a gaban wasu gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jam'iyyar a mazaɓar Sarkin Yara da ke mahaifarsa Daura a jihar katsina da ke arewacin kasar.
Baya ga sabunta rijistar zama mamba na jam'iyyar APC, Shugaba Buhari, ta hanyar sakon da kakakinsa Malam Garba Shehu ya aike wa maneman labarai, ya yi wasu kamalai.
Ga abubuwa biyar da shugaban kasar ya fada a yayin ziyarsa ta Daura:
Rijista daga ƙasa zuwa sama

Asalin hoton, Twitter/@Bashirahmaad
Shugaba Buhari ya yi kira ga mambobin APC tun daga mataki na mazaɓa zuwa ƙaramar hukuma da jihohi 36 tare da birnin tarayya da kuma tarayya su fito su yi sabuwar rijistar jam'iyyar.
Ya ce mallakar jam'iyyar ga mambobinta shi zai ƙarfafa tsarin APC tare da tabbatar da kyakkyawan fata a zaɓuka da kuma makomarta.
Ku yi hankali da cutar korona

Asalin hoton, OTHER
A yayin da shugaban ya yi kira ga dukkan masu sha'awar jam'iyyarsa su yi fitar dango domin sabunta rijistarsu, ya hore su da su bi ka'idojin kiyaye kamuwa da cutar korona.
Sai dai a yayin da ya yi rijsta sanye da takunkumi, Shugaba Buhari ya cire takunkumin daga bisani lamarin da wasu ke ganin tamkar ya karya dokar da ya sanya ce ta wajabta sanya takunkumi a bainar jama'a.
A makon jiya ne shugaban kasar ya amince a yi daurin wata shida ga duk mutumin da aka samu da laifin kin sanya takunkumi a bainar jama'a.
Aiwatar da kasafin kudin 2021
Shugaba Buhari ya yi wa 'yan kasar alkawarin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021 ba tare da kumbiya-kumbiya ba.
"Mun bai wa dukkan ma'aikatun gwamnati umarnin bin abubuwan da ke cikin kasafin kudin yadda majalisun dokokin tarayya za su goyi bayanmu cikin sauki a kasafin kudi mai zuwa. Za mu iya gama musu abin da muka karba da kuma yadda muka kashe shi," a cewar shugaba Buhari.
Mayar da hankali a fannin noma
Shugaban Najeriya ya jaddada ikirarin da ya yi cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen inganta fannin noma domin yalwata hanyoyin bunkasa tattalin azikin kasar.
A cewarsa: "Muna ci gaba da godiya ga kasar Morocco bisa goyon bayan da ta ba mu wajen samar da takin zamani a kasar nan.Yanzu muna da kwamfanonin yin takin zamani 42 da ke samar da takin zamani a shiyya shida."
Sako ga masu fada a ji
Kazalika shugaban Najeriya ya yi kira ga masu fada a ji a kasar su yi tunani da kuma adalci a yayin da suke sharhi kan gwamnatinsa, yana mai cewa ya kamata su rika yaba masa kan ayyukan da ya aiwatar.
"Ina so masu fada a ji namu su kasance masu nazari da kuma tuna cewa mun karbi mulki ne a 2015. Su tuna halin da muke ciki a wancan lokacin, da kuma kudin da ake da su a lokacin da kuma ayyukan da muka taras.
"Daga shekarar 1999 zuwa 2014, kasarmu ta fitar da gangar man fetur 2.1m kuma ana sayar da kowacce ganga a kan fiye da dala 100a wasu lokuta. Tattalin arzikinmu ya fi shiga mummunan hali a lokacin da muka zo hakan ne ya sa muka ceto wasu jihohi daga durkushewa ta yadda za su iya biyan albashi da fansho. Yanzu al'amura sun fi daidaita," in ji shi.
Karin labarai da za ku so ku karanta:











