Miyetti Allah: Abin da aka tattauna a babban taron kungiyar Fulani

Bayanan sautiTattaunawar BBC da Shugaban Ƙungiyar Fulani makiyaya ta 'Mi Yetti Allah' a Najeriya

Ƙungiyar Fulani makiyaya ta 'Mi Yetti Allah' ta gudanar da wani babban taro na yini guda a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ƙusoshin kungiyar suka tattauna kan ƙalubalen da makiyayan ke fuskanta dangane da matsalar tsaron da ake fama da ita a ƙasar.

Shugabannin ƙungiyar na ƙasar da kuma Uban ƙungiyar, mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'adu Abubakar, duka sun halarci taron.

Muhammadu Kiruwa, shugaban kungiyar Fulani makiyayan ta 'Mi Yetti Allah' na kasa ya shaida wa BBC cewa a taron an cimma matsayar tattara bayanan matsalolin da Fulani ke fuskanta da kuma cin zarafin da ake yi musu.

"Dole ne a dawo da hankalin mutane cewa su kansu al'ummar Fulanin ba su tserewa ta'addanci da ta'addancin ƴan ta'adda ba," in ji Ƙiruwa.

Ya ce sun ɗauki matakin ci gaba da wayar da kan al'ummar Fulani ganin cewa ba duka al'ummar Fulanin ne ke cikin ƙungiyar ta Mi Yetti Allah ba.