Boko Haram: Ƙarin 'yan matan Chibok sun tsere daga daji

Asalin hoton, EPA
Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa karin 'yan matan da aka sace daga makarantar Chibok a 2014 sun tsere daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Mahaifin wata tsohuwar dalibar Chibok din ya shaida wa BBC cewa ya yi magana da 'yarsa wadda ta tsira.
Ya ce sun yi magana da ita ta waya bayan da suka kubutu inda take ta kuka.
Bayanai na cewa ita da wasu da aka sace a Chibok da kuma wasu yankunan sun tsere ne bisa dukkan alamu saboda farmakin da sojoji suke kai wa 'yan Boko Haram.
Matan sun tsira ne kwanaki kadan bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar.
A shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka kai hari a makarantar mata ta Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya inda suka sace dalibai 276.
Gangami da kiraye-kiraye

Asalin hoton, AFP
Lamarin ya janyo suka ga gwamnatin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan daga fadin duniya inda aka kirkiro maudu'in #BringBackOurGilrs domin matsa lamba ga gwamnatin ta ceto matan.
Fitattun mutane a fadin duniya ciki har da mai dakin tsohon shugaban Amurka Michaelle Obama sun yi ta matsa lamba kan gwamnatin wancan lokacin domin ganin ta ceto 'yan makarantar ta Chibok.
Sai dai gwamnatin Muhammadu Buhari ta ceto galibinsu bayan ya yi nasara a zaben 2015 har ma sun gana da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja.
Sai dai har yanzu ana kira ga shugaban da ya ceto sauran 'yan matan.











