Matsalar Tsaro: Yadda aka yi garkuwa da mutum 30 a Birnin Gwari

Rahotanni daga jihar kaduna da ke arewacin Najeriya na nuna cewa an kai hari ƙauyen Kungi da ke yankin Birnin Gwari da safiyar yau Alhamis.
Ana tunanin an yi awon gaba da mutane sama da 30 a harin sannan mutum ɗaya ya rasa ransa.
Har yanzu hukumomin jihar Kaduna ba su ce komai ba dangane da wannan harin.
Sai dai wani mazunin ƙauyen wanda bai amince a ambaci sunasa ba ya shaida wa BBC cewa "maharan sun faɗa cikin gidan mutane su kara wa mutum bindiga, sai su ce mu tafi," a cewarsa.
Ya ce mutumin da aka kashe ya yi wa maharan gardama ne, ya nuna masu ba zai bi su ba shi ya sa suka harbe shi.
Ganau din ya bayyana cewa cikin wadanda aka sace akwai maza da mata har ma da ƙananan yara. Ya ce har da jikokinsa guda uku a cikin mutanen.
"Ɗiyata ce ta haife su, su ma suna cikin mutanen da aka tafi da su" kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana cewa garin Kungi na nan a cikin zaman ɗar-ɗar saboda abin da ya faru.
"Muna cikin wani hali a yankin Birnin Gwari. Mun miƙa komai wurin Allah saboda tashin hankalin ya ishe mu. Bala'i ya kai bala'i," in ji shi.
Sai dai ya ce akwai jami'an tsaro da dama a gaba ɗaya yankin na Birnin Gwari amma zaman su bai hana ayyukan masu garkuwa da mutane ba.
Mutumin ya ce ko da maharan suka shigo garin sun yi tunanin sojoji ne saboda irin bindigogin da suka riƙe, sai daga baya suka fahimci ashe ƴan bindiga ne.
Ya ce su yanzu kawai sun sa wa ransu Allah ne ke kare su.
Ya bayyana cewa a halin yanzu Garin Birnin Gwari na cike da ƴan gudun hijira manya da yara daga ƙauyuka da ke yankin saboda zaman ƙauyen ya gagare su.
Yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ya daɗe a halin rashin tsaro na hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Dubban mutane ne ke tserewa daga kauyuka daban-daban na yankunan kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari inda suke neman mafaka a garin Buruku na jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
A hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu a 'yan kwanakin nan, al'amarin ya yi sandin asarar rayuka da raunata mutane da dama, baya ga awon gaba da ake zargin maharan sun yi da mutane da kayayyaki.











