Yadda dakarun Mali suka kashe ƴan tada ƙayar baya sama da 100

Mali

Sojoji a Mali sun ce sun kashe masu ikirarin jihadi dari a wani farmakin hadin gwiwa da suka yi da sojojin Faransa.

A cikin wata sanarwa, rundunar sojan ta Mali ta ce an sake kame wasu masu kishin Islama ashirin a wannan samamen, wanda aka gudanar a cikin watan Janairu.

Mayakan suna iko da manyan yankuna na yankin Sahel.

Tun lokacin da fitinar ta ɓarke a arewacin Mali a cikin 2012 tashin hankali ya bazu zuwa makwabtan ƙasar da suka hadar da Nijar da Burkina Faso.

Faransa na da sojoji sama da dubu biyar a yankin a wani bangare na wani dogon aiki da aka shirya don dakatar da tashin hankalin da masu kaifin kishin Islama ke haifarwa

Wannan lokacin musamman a hannun ƙungiyar IS reshen Greater Sahara da ake kira (ISGS), wadda ke iƙirarin mubaya'a ga ƙungiyar Gabas ta Tsakiya.

A shekarar da ta gabata, a ranar 30 ga Satumba kusan sojoji 85 ne suka mutu lokacin da ISGS ta mamaye sansaninsu da ke Boulikessi a kan iyakar Burkina Faso.

Sannan a ranar 1 ga watan Nuwambar 2019, ƙarin mutum 49 aka kashe a wani hari da ISGS ta kai kan wani sansani a Indélimane da ke kusa da iyaka da Nijar a gabashin ƙasar mai nisa.

Rashin horo da ƙarancin makamai na daga cikin abubuwan da suka janyo koma-baya a yaƙi da matsalolin tsaro a Mali.

Amma akwai ƙarin fargaba kan rashin jagoranci na gari ta fuskar siyasa daga tsohon Shugaba Keita a Bamako da kuma batun cewa gwamnati ta yi sake wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015 da 'yan a-waren Tuareg da ke arewacin ƙasar.

Jinkirin da aka yi wajen murƙushe mayaƙan da kuma raba iko da kuɗi zuwa ga matakin yanki ya haifar da yanayin takaici da ta'addanci zai ci gaba.