Sophie Pétronin: Ana fatan sakin 'yar Faransa da masu garkuwa suka sace

'Yan uwan Sophie Pétronin sun yi bakin ƙoƙarinsu don ganin jama'a ba su manta da sace ta ba

Asalin hoton, Liberons Sophie/Facebook

Bayanan hoto, 'Yan uwan Sophie Pétronin da masu fafutika sun yi bakin ƙoƙarinsu don ganin jama'a ba su manta da sace ta ba

Sophie Pétronin mai shekara 75, an sace ta a Mali a shekarar 2016 kuma kusan shekara shida kenan ana ganin ita kaɗai ce 'yar Faransa da ta yi saura a hannun masu garkuwa a faɗin duniya.

Rahotanni na nuna cewa za a sake ta tare da wani shahararren ɗan siyasar Mali, Soumaïla Cissé, a matsayin musaya da fursunonin masu iƙirarin jihadi fiye da 100.

An yi garkuwa da Soumaïla Cissé mai shekara 70 a watan Maris.

Ana zargin wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi mai alaƙa da al-Qaeda ta JNIM da sace mutanen biyu.

Abin da muka sani zuwa yanzu

Mahukunta shun daɗe suna neman kuɓutar da ita, sai dai suna ɗariɗari da abin da ka iya faruwa a mintunan ƙarshe.

"Ya yi wuri mu fara murna," a cewar ɗan Pétronin mai suna Sébastien Chadaud. "Mun shafe shekara huɗu a cikin wannan yanayin."

Mista Chadaud na kan hanyarsa ta zuwa Bamako, a cewar wani ɗan uwansa ranar Talata.

Rahotanni daga Mali sun bayyana cewa kusan 'yan bidniga 100 aka saka a 'yan kwanakin nan a cikin shirin musayar fursunonin.

Daga baya sun bayyana a garin Tessalit, inda rahotanni ke cewa a nan aka sace Sophie Pétronin da Soumaïla Cissé.

Ƙungiyar JNIM ta yi iƙirarin cewa dakarunta 206 aka saka, a cewar shafin kafar Nouvel Horizon.

Wace ce Sophie Pétronin?

An kusa mantawa da Sophie Pétronin bayan masu iƙirarin jihadi su sace ta duk da ƙoƙarin 'yan uwanta na yayata lamarin.

Wadda aka sace ta ranar jajiberin Kirsimetin 2016 a garin Gao, ta shahara garin sakamakon aikin agajin da take yi na taimaka wa yaran da ke fama da yunwa.

Ta yi ta gudanar da ayyukan agaji a ƙarƙashin ƙungiyar Association Aid tun 2004 kuma ƙwararriya ce kan cutar kurkunu, wadda ake samu nta hanyar gurɓataccen ruwan sha a arewacin Mali.

Bayan Buzaye 'yan tawaye sun ƙwace garin Gao a shekarar 2012, an yi gwarkuwa da jami'an difilomasiyyar Aljeriya bakwai kuma ofishin Aljeriyar ne ya ba ta mafaka kafin a kai hari kan ginin.

Ta tsere ta ƙofar baya kuma an fice da ita daga Mali sanye da dogayen kaya.

"Mun tsallake sahara a dare ɗaya maimakon kwana biyu da aka saba," ta faɗa wa jaridar Le Dauphiné Libéré a 2012. "Da na duba ma'\aunin gudu a mota, mun riƙa tafiya a kilomita 130 duk sa'a ɗaya.

Ɗan Sophie Pétronin ya ce ya yi wuri su fara murna har sai an tabbatar da sakinta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan Sophie Pétronin ya ce ya yi wuri su fara murna har sai an tabbatar da sakinta

Ta tsere daga Mali a asirce amma ta koma, inda aka sace ta da tsakar rana a wani hari da ƙungiyar JNIM ta yi iƙirarin kaiwa.

Ta bayyana a wani bidiyo sau biyu kuma ɗanta har ya haɗu da wani mai shiga tsakani, wanda ya ce 'yan bindigar sun yarda su karɓi kuɗin fansa.

A ɗaya daga cikin bidiyon a 2018, cikin gajiya da sanyin rai ta nemi agaji daga Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Tana fama da cutar daji da malaria a lokacin da aka yi garkuwa da ita.