Bah Ndaw da Assimi Goita ne za su jagoranci Mali zuwa lokacin zabe

Bah Ndaw, sanye da fararen tufafi, ya sha rantsuwar kama aiki a Bamako babban birnin kasar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bah Ndaw, sanye da fararen tufafi, ya sha rantsuwar kama aiki ranar Juma'a a Bamako babban birnin kasar
Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon ministan tsaro na Mali Bah N'Daw shi ne wanda aka rantsar a matsayin sabon shugaban riƙon ƙwarya a Mali, makonni biyar bayan hamɓarar da Ibrahim Boubacar Keita.

Sabuwar gwamnatin da aka kafa za ta jagoranci ƙasar na watanni 18 har zuwa lokacin da za yi zaɓe a ƙasar.

Wanda ya jagoranci juyin mulki a ƙasar, Kanal Assimi Goita ne ya zaɓe shi domin jagorantar gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar.

Kanal Goita ɗin ne zai kasance mataimakin Mista Ndaw mai shekara 70.

Naɗa farar hula a matsayin shugaba na daga cikin sharuɗan da ƙungiyar yammacin Afirka ta gindayawa ƙasar kafin ta dage takunkumi da ta ƙaƙabawa ƙasar bayan juyin mulki.

Harkokin kasuwanci ya tsayar cak a birnin Bamako, yayin da ake jiran sanarwar Ecowas bayan rantsar da sabon shugaban ƙasar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Wane ne Janar Bah N'Daw?

An haifie tsohon soja a ranar 23 ga watan Agustan 1950 a yankin Segou.

Yana da shaidar karatu a fanin soji daga Faransa da wata shaidar makarantar yaki ta CID a 1994. Yana da kwarewa sosai a fanin sojin sama.

Tsohon ministan tsaron da harkokin cikin gida ya fito ne daga rukuni na 7 na 1973 daga makarantar dakarun hadin-gwiwa (EMIA), da ke Koulikoro.

Bayan ya kammala karatu ya shiga soji a matsayin mai bada taimakon sa kai a 1 ga watan Yuni, 1973.

Da shekara ta zagayo sai aka zabe shi domin yin kwas kan tuka helikwafta ga USSR.

Bah Ndaw work as defence minister under Ibrahim Boubacar Keïta

Asalin hoton, AFP

A ranar 27 ga watan Maris din 2014, tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya nada shi Ministan harkokin tsaro da tsoffin sojoji.

Kanar-Manjo Bah N'Daw, da abokansa ke kira "the great" saboda tsayinsa (1.95 m), tsohon matukin helikwafta ne kuma ya taba zama mataimaki da Janar Moussa Traoré.

Daga 2008 zuwa lokacin ritayarsa a 2012, Kanar-Manjo Bah N'Daou shi ne daraktan tsoffin sojoji na kasa da wayanda yaki ya shafa.

Manjo Janar Bah N'Daw jami'in sojin kasa ne daya sha karbar manyan kyaututuka na soji da na ƙasa.

Ana dai bayyana shi a matsayin mai jajircewa da hazaka a fanin aikin soja.

French Defense Minister Jean-Yves Le Drian and im Malian counterpart Bah N'Daw pose on July 16, 2014 in Bamako

Asalin hoton, Getty Images

Me ya faru a Mali?

A ranar Talata ne dai sojojin ƙasar Mali suka tilasta wa Tsohon Shugaba, Ibrahim Boubacar Keïta yin murabus.

Sojojin da suka hamɓarar da Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta sun bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin gudanar da sabon zaɓe a ƙasar.

Wannan ya biyo bayan bayyanar shugaban a kafar talabijin, inda ya ce ya sauka daga muƙaminsa.

Sojojin sun yi awon gaba da shi tare da firaministansa daga babban birnin ƙasar zuwa wani sansanin soja da misalin karfe 4:30pm agogon ƙasar.

Ita ma ƙungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin daɗinta bisa wannan lamarin, inda ta ce ta dakatar da ƙasar ta Mali daga cikin ƙungiyar ta ECOWAS.

Ƙasar ta jima cikin rikicin siyasa inda aka rinƙa zanga-zangar neman shugaban ƙasar ya sauka daga mulki saboda hare-hare ƙungiyoyin jihadi da matsalolin rashawa da suka durkushe tattalin arziki.

A wata tuntubar juna a makon da ya gabata, wasu daga cikin sharaudan naɗin sabon shugaban da aka gindaya sun hada da dole ya kasance dan asalin Mali, shekarunsu ya soma daga 35 zuwa 70, sannan ya kasance mai gaskiya da ɗa'a.

Sannan ba a taba samun sa da aikata babban laifi ba.

Sannan dole Firaministan da mambobin gwamnatin rikon su kasance sun cike wannan sharuɗa irin na shugaban ƙasar.

A taronsu karo na 57, da suka gudanar 7 ga watan Satumba, 2020 a birnin Yamai na Nijar, Ecowas ta bai wa rundunar sojin junta wa'adi zuwa 15 ga watan Satumba domin mika mulki ga farar hula.