Juyin mulki a Mali: Dubun dubatar mutane sun yi murnar cire Ibrahim Boubacar Keïta

Asalin hoton, Getty Images
Dubun dubatar mutane sun famtsama kan titunan Bamako babban birnin Mali domin yin murnar kawar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta.
Sojojin da suka yi juyin mulki sun kama Mr Keïta ranar Talata sannan suka tilasta masa ajiye mulki, lamarin da ya jawo musu allawadai daga fadin duniya.
Da ma Mr Keïta ya fuskanci tarzoma daga wurin 'yan kasar gabanin kama si kuma 'yan kasar ta Mali sun yi maraba da cire shi.
Dubun dubatar mutane sun taru a dandalin Independence da ke Bamako suna busa sarewa, inda wasu suka rika cewa sun yi nasara kan tsohon shugaban kasar.
"Ina matukar farin ciki, mun yi nasara. Mun zo nan ne domin mu gode wa dukkan jama'ar Mali saboda nasara ce ta jama'a," in ji Mariam Cissé, wani magoyin bayan 'yan hamayya, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
"IBK ya gaza," a cewar wani tsohon soja Ousmane Diallo.
Sai dai ya gargadi sojoji su bi a hankali, yana mai cewa "ya kamata soji su guji tunanin cewa sun zo ne su zauna a kan mulki".
Tun da fari, jami'an hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya sun gana da tsohon shugaban ƙasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da sauran jami'an gwamnatinsa da aka tsare a farkon watan nan bayan da sojojin juyin mulki suka ƙwace iko.
Tun ranar Talata ba a ji daga bakin Keita ba, duk da cewa dai wani mai magana da aywun ɓangaren 'yan hamayya na Mali ya ce ana tsare da tsohon shugaban ne a sansanin soji da ke garin Kati, a wajen birnin Bamako, kuma sanin abin da zai same shi ya ta'allaƙa ne kan abin da mutanen ƙasar suka shirya.
Gani na ƙarshe da aka yi wa hamɓararren Shugaba Ibrahim Boubacar Keita shi ne ranar Talata a wani jawabi da ya gabatar a gidan talbijin, inda ya sauke majalisar dokoki tare da sanar da yin murabus ɗinsa, bayan da sojoji suka ɗauke shi zuwa barikin Kati.
Duk da cewa tawagar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta gana da shi da sauran jami'an da ke tsare, shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Mali MINUSMA, bai yi wani ƙarin bayani kan yanayin da shi da mutanen ke ciki ba.
Sojoji za su naɗa gwamnatin rikon-ƙwarya
A ranar Alhamis da dare ne sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Mali suka ce za a naɗa gwamnatin rikon-ƙwarya, wadda za ta kasance wataƙil daga cikin farar-hula ko sojoji.
A ranar Talata aka tilasta wa Ibrahim Boubacar Keïta murabus bayan yi masa juyin mulki.
Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun buƙaci a mayar da shi mulki sannan Majalisar Dinkin Duniya ta ɓukaci a saki jami'an da ake tsare da su.
Sai dai sojojin da suka jagoranci juyin mulkin sun ce suna tuntuɓar juna da ƴan hamayya da sauran ƙungiyoyi a ƙoƙarin kafa gwamnatin riƙo.
Sun ce za a gudanar da zaɓe a cikin lokacin da ya dace kuma sun alƙawarta mutunta yarjejeniyar ƙasashen duniya kan yaƙi da mayaƙan jihadi.
Gamayyar ƴan hamayya, da suke ta gangamin ganin Mista Keïta ya sauka, sun yi kira da a gudanar da gangamin murnar murabus ɗin shugaban a ranar Juma'a.
A ranar Alhamis, ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka wato ECOWAS, ta ce za ta tura wakilanta domin tabbatar da mayar da doka da oda ƙarƙashin kundin tsarin mulki.
Akwai ƙarin jami'an sojoji a wajen ma'aikatun gwamnati a birnin Bamako, sai dai shaguna da wuraren sana'o'i sun kasance a buɗe.
Mali tana da faɗi kuma ta haɗa iyaka da ƙasashen yankin Sahara, tana cikin matalautan ƙasashe a duniya sannan ta sha ganin irin wannan juyin-mulkin. Yanzu haka tana fama da hare-haren ƙungiyoyin jihadi da fitintinun ƙabilanci.
Mista Keïta ya yi nasara zaɓe a karo na biyu a 2018, amma tun daga watan Yuni ya ke fuskantar gagarumin bore da zanga-zanga kan rashawa, rashin tattalin arziki da rigingimu kan zaɓen ƴan majalisa.
Sannan akwai fushin da sojoji ke nuna wa kan rashin albashi da yaƙin da suke da mayaƙan jihadi.
''Za mu kafa kwamitin riƙon ƙwarya, da shugaban riƙon ƙwarya wanda zai kasance soja ko farar-hula," a cewar kakakin Junta, Kanar Ismaël Wagué a tattaunawarsa da tashar talabijin France 24.
"Muna tuntubar juna tsakanin mu da ƙungiyiyon farar-hula, jam'iyyun adawa, masu rinjaye da sauran al'umma a ƙokarin ganin mun kafa gwamnatin riƙo.''
Za mu tabbatar ''mun gaggauta kafa gwamnatin'', a cewarsa.

Ƙarƙashin matsi, jagororin juyin-mulkin na da mabambantan ra'ayi
Mary Harper, Editan Afirka, BBC World Service
Sojojin da suka ƙwace mulki a Mali sun ce suna tattaunawa da jam'iyyun adawa da sauran ƙungiyoyi a ƙoƙarin kafa gwamnati.
Duk da irin kiraye-kiraye masu ƙarfi daga shugabannin yankin Afirka da ƙetare kan dawo da shugaban da aka hamɓarar Ibrahim Boubacar Keïta kujerarsa, wayanda suka jagoranci juyin-mulkin da ƴan adawa na nuna turjiya.
Suna son mahukunta da za su iya yaƙar rashawa, farfado da tattalin arziki da kawo ƙarshen ƙabilanci da rikicin jihadi.
Abin ya zo da mamaki, musamman ganin yadda ƙasashe duniya suka gaggara shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin siyasar ƙasar.

Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka na yi wa sojoji matsin lamba,ta yi barazanar ƙaƙabawa wa sojoji takunkumi idan suka ƙi miƙa mulki ga farar hula.
Ƙasashen duniya da dama sun yi Allah-wadai da juyin mulkin, inda ake bayyana damuwa kan yiyuwar ƙazancewar rikici a Mali.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar hadin-kan ƙasashen Afirka sun ce juyin mulki ''abu ne da aka yi a zamanin baya don haka ba za su amince da hakan ba''.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce ƙasar sa da Jamus sun yi alla-wadai da juyin mulki don haka sun bukaci a gaggauta miƙa mulki ga farar hula.
Faransa, wacce ta mulki Mali, akwai dubban dakarunta a Mali da ke yaƙar ƙungiyoyin jihadi kuma ministan sojin ƙasarta Florence Parly ta aike sakon tuwita cewa za su cigaba da ayyukansu a ƙasar.













