Juyin mulkin Mali: Ecowas na son a mayar da Boubacar Keïta kan mulki

Malian Air Force deputy chief of staff Ismael Wague (front row 2nd L) speaks during a press conference in Kati, Mali on August 19, 2020.

Asalin hoton, AFP

Shugabannin kungiyar kasashen Yammacin Afirka sun yi kira a mayar da shugaban da aka kora daga kan mulki a Mali, Ibrahim Boubacar Keïta, kan kujerarsa.

Kungiyar Ecowas ta ce za ta aika wakilai kasar domin su tabbatar an dawo da tsarin mulki.

Hakan na zuwa ne bayan Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira a saki dukkan jami'an gwamnatin da aka tsare.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi makamancin wannan kira na gaggauta sakin dukkan jami'an gwamnati da kuma mayar da gwamnatin da tsarin mulki ya amince.

Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta bi sahun masu yin alla-wadai da juyin mulkin sojiojin na Mali, da ya yi sanadin tilasta wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta sauka daga mulki.

A ranar Alhamis ne kuma shugabannin sojin da suka yi juyin mulki suka tattauna da shugabannin 'yan hamayyar kasar wadanda suka yi maraba da tumbuke gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta.

Sun dora masa alhakin gaza dakatar da hare-haren masu ikirarin jihadi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar a kansa.

Gamayyar 'yan hamayyar ta ce ta yaba da kishin da sojin suka nuna wajen son kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula.

Ranar Alhamis shugabannin ƙasashen Afrika Ta Yamma suka tattaunawa ta bidiyo kan juyin mulkin Mali.

"Mun yanke shawarar cikin gaggawa mu tura tawaga mai karfi domin ta tabbatar da dawo da tsarin mulki nan take," a cewar kungiyar mai mambobi 15 a karshen taronta na yau.

"Muna kira a dawo da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta kan kujerarsa ta shugabancin kasa," in ji sanarwar da shugaban Ecowas wanda kuma shi ne shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou, ya karanta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari awata sanarwa ya ce Mali "ta tsunduma cikin rikicin siyasa" wanda zai "iya yin tasiri sosai a kan kasar ta Mali da kuma kasashen yankin".

line

Rufe kan iyakoki

Ƙungiyar ta sanar da rufe kan iyakokinsu da Mali da jingine duk wasu harkokin kuɗi da korarta daga hukumomin zartar da al'amura.

Faransa ta ce za ta ci gaba da ayyukanta na soji kan masu da'awar jihadi a Mali, duk da hamɓare tsohon shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar Keita.

Ita ma Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali, tana cewa juyin mulki wani abu ne tsohon yayi da ba za a sake lamuntarsa ba.

Me sojojin suka ce?

Colonel Assimi Goita speaks to the press at the Malian Ministry of Defence in Bamako, Mali, on August 19, 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Col Assimi Goita shi ne yake shugabantar sojojin

Sojojin da suka hamɓaras da gwamnatin Mali a wani juyin mulki sun faɗa a ranar Laraba cewa babban abin da suka fi damuwa da shi, shi ne tabbatar da zaman lafiya amma ba mulki ba.

Wani Kanar na rundunar sojin kasar, Assimi Goita, ya ce shi ne shugaban mulkin sojin.

Ya yi kira ga ma'aikata su koma bakin aiki.

Sun yi alƙawarin gudanar da sabbin saɓuka a wani abu da suka kira cikin gwargwadon lokaci.

Sun zargi Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da barin Mali ta tsunduma cikin hargitsi da zaman kara-zube.

Ibrahim Boubacar Keïta ya lashe zaɓe a wa'adi na biyu cikin 2018, sai dai tun daga watan Yuni yake fuskantar gagarumar zanga-zanga a kan tituna dangane da cin hanci da rashin iya gudanar da tattalin arziƙi da kuma taƙaddama kan zaɓukan majalisa.

line
Rikicin kasar Mali ya dade yana ruruwa shi ya sa mutane ba su yi mamaki ba da aka ture gwamnatin Keita
Bayanan hoto, Rikicin kasar Mali ya dade yana ruruwa shi ya sa mutane ba su yi mamaki ba da aka ture gwamnatin Keita