Ilimi a Kano: Dalilan dakatar da ciyar da daliban jihar

Yara na kaurace wa makaranta saboda dakatar da shirin ciyarwa a makarantun firamare

Asalin hoton, FACEBOOK/SALIHU TANKO YAKASAI

"Gaskiya rashin ciyarwar ya gurgunta mana zuwan yara (makaranta), domin idan akwai abinci to yara suna zuwa ba ma sai an ce su je ba," in ji wani malamin makarantar firamare a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

An dakatar da ciyarwar ne tun gabanin rufe makarantu sanadiyyar cutar korona.

BBC ta tattauna da wani dalibi a makarantar firamaren gwamnati da ke cikin garin Kano, inda ya ce 'Tunda aka je hutun korona ba a ba mu (abinci), kuma ko da aka dawo ma ba a kara ba mu ba.'

Gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta bullo da tsarin ciyarwar a matsayin wani mataki na cika alkawarin da ta dauka gabanin zaben shekara ta 2015.

Tun bayan fara shirin wasu gwamnatocin jihohi su ma sun bi sahu, inda suke gudanar da irin wannan shiri na ciyarwa a wasu makarantun gwamnati.

Malamai na damuwa kan tsayar da shirin ciyar da yara 'yan makaranta

Ko da yake hukumomin na alfahari da shirin, amma dakatar da shi ya fara jefa iyayen yaran da ma daliban cikin damuwa.

"Ina so a ci gaba da ciyarwa saboda mu rinka jin mu da kuzari koda an yi aiki mai yawa."

A shekara ta 2019 ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da ciyarwar, wadda a wancan lokaci aka ce za ta gudana a makarantun firamare 6,800 na fadin jihar Kano.

A cewar gwamnan an fito da shirin ne a matsayin wani bangare na samar da ilimi kyauta ga yara, da masu karamin karfi, da kuma bunkasa ilimin yara mata.

A wasu makarantun firamare da BBC ta ziyarta ta tabbatar da dakatar da ciyarwar, wani abu da malaman suka bayyana a matsayin daya daga cikin manyan dalilan da suke hana yara zuwa makaranta a yanzu.

Gwamnatin tarayya ce ta kirkiro da shirin ciyarwa amma gwamnatocin jihohi sun bi sahu

Asalin hoton, FACEBOOK/SALIHU TANKO YAKASAI

BBC ta tattauna da kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Kiru, wanda ya tabbatar da dakatar da ciyarwar, sai dai ya ce an yi hakan ne domin tsayawa a yi gyara ga yadda shirin ke gudana.

Ya ce bayanan da ake amfani da su a baya a shirin ciyar da yara na gwamnatin tarayya ya nuna cewa ana gudanar da shi ne a kan yara miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da hamsin, sai dai a halin yanzu yaran da ya kamata su ci gajiyar shirin ('yan aji daya zuwa 3) sun kai sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara da hamsin.

Sai dai kwamishinan bai bayar da hujjar dakatar da shirin ciyar da ɗaliban karkashin gwamnatin jiha ba.

Wannan rahoto ne na musamma da BBC Hausa ta kawo maku tare da tallafin gidauniyar .