Abin da ya sa muke son yi wa dokar Masarautun Kano ta 2019 kwaskwarima - Gwamnati

Asalin hoton, FACEBOOK/KANO STATE GOVT
A mako mai zuwa ne ake sa ran majalisar dokokin jihar Kano za ta dauki matsaya kan bukatar da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar mata na yin gyara ga dokar Masarautun Kano ta 2019.
A farkon makon ne gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar wa Majalisar Dokokin jihar bukatar yi wa dokar Masarautun jihar ta 2019 kwaskwarima, don ganin an kara Sarkin Dawaki Babba a cikin masu zaben Sarkin Kanon.
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban Majalisar Dokokin jihar Abdul'aziz Garba Gafasa ya karanta takardar a yayin zaman majalisar.
Matakin na zuwa ne a yayin da Masarautar Kano take jiran amsar gwamnati a hukumance kan bukatar nada Alhaji Aminu Babba Danagundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba da kuma Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano
Marigayi Sarkin Ado Bayero ne ya sauke Aminu Babba daga sarauta, yayin da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sauke Lamido Ado Bayero.
Aminu Babba, ya kalubalanci sauke shi da a kotu, amma Kotun Ƙoli ta tabbar da sauke shi bayan shekara 17 ana shari'a.
Wasu dai na ganin yunkurin mayar da mutanen biyu masarautar Kano yana da alaka da siyasa, kuma zai rage kimar masarautar. To sai dai gwamnatin Kano na musanta wannan ikirari.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano a arewacin Najeriya Malam Muhamamd Garba, ya ce kasancewar girman sarautar Sarkin Dawaki Babba da Masautar Kano ta kirkiro ya sa gwamnati ta ga dacewar sanya ta cikin masu zaben Sarkin Kano.
A yayin da yake yi wa BBC karin bayani, Malam Muhammad Garba ya ce, sabanin yadda wasu ke yadawa cewar gwamnati na ƙoƙarin yi wa hukuncin da Kotun Ƙoli ta yi karan tsaye, kan tabbatar da tuɓe rawanin da marigayi Sarkin Kano ya yi, ya ce gwamnatin jihar ta mutunta hukuncin kotun
Muhammad Garba ya ce hakan ne ma ya sa gwamnati ta ga dacewar mayar da shi cikin masu zaben sarki ta wata hanyar daban, don kaucewa saba wa kotu, wanda hakan zai kawo ci gaba ga masarautar a cewar.
Har ila yau majalisar dokokin ta Kano ta bakin shugaban masu rinjaye, Hon Kabiru Hassan Dashi ta tabbatar wa BBC cewar sun sami kwafin takardar da gwamnan ya aike musu, kuma har an karanta ta a gaban majalisa sannan ana sa ran ci gaba da tattaunawa kan bukatun da ke cikin takardar a mako mai zuwa.

Yadda zaben sarki yake tun asali a Kano

Asalin hoton, FACEBOOK/ADO BAYERO MEMORIAL
To sai dai masana tarihi irin su Malam Ibrahim Hussaini da ke Kano, na da ra'ayin cewar ko kadan wannnan mataki na gwamnati bai kamata ba, saboda dukkan wadanda suke zabar sarki na da irin gudunmuwar da suka bayar da har ta kai su ga samun wannan matsayi, musamman lokacin yakin kafa Daular Usmaniyya ta Shehu Dan Fodiyo.
Wani bincike ya nuna cewar a kan sami bambancin sauyin wadanda ke zaben sarki a Kano, a inda a zamanin sarakuna Hausawa, Shamaki da Dan Rimin da limamin Kano su ne ke zaben sarki, kuma a kan samu sauyi kan hakan lokaci zuwa lokaci.
Masu zaben sarkin ba su tabbata a matayin da suke ba na mutum hudu ba har sai a zamanin mulkin Fulani a Kano inda suka hada da Madaki daga Fulanin Yolawa, sai Sarkin Bai daga Fulanin Dambazawa, Sarkin Dawaki Mai Tuta daga Fulani Sullubawan Tuta karkashin Malam Jamo, sai kuma Makaman Kano daga Fulanin Jobawa.
Duka wadannan gidaje sun taka muhimmiyar rawa a lokacin jihadin kafa daular Fulani.
Abun jira dai yanzu a gani shi ne ko majalisar ta Kano za ta amince da wannan bukata da gwamnan na Kano ya aike mata, ko kuma a'a.
Karin labaran da za ku so ku karanta











