Masarautar Kano: An tsunduma ta cikin siyasa – Masana Tarihi

Asalin hoton, Facebook/Salihu Tanko Yakasai
Masana tarihi a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun fara tsokaci kan sake nadin da sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi wa Aminu Babba dan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba kuma dan majalisar sarki.
A ranar Litinin ne masarautar ta fitar da sanarwar bayar da sunansa domin sake nada shi hakimi, bayan cire shi shekara 17 da suka gabata.
A shekarar 2003 ne Ado Bayero ya sauke Aminu Babba daga sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma Hakimin Gabasawa sakamakon bijire wa umarnin da ya ba shi na bayyana a gabansa.
A baya ma tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya sauke Sanusi Lamido Ado Bayero da ke riƙe da muƙamin Ciroman Kano saboda ya ƙi yi masa mubaya'a bayan zamansa sarkin Kano.
Sabon abu ne a tarihin Masarautar Kano
Dr. Tijjani Mohammad Naniya, wani masanin tarihi da ke jami'ar Bayero ta Kano, ya bayyana wa BBC cewa a tarihance ba a mayar da wanda sarki ya cire daga sarauta.
Ya ce wannan matakin ya yi wa Masarautar Kano illa babba saboda "duk wanda ya gaji sarauta cewa ake ya gaji Dabo, ya gaji Rumfa, ya gaji dukkan iyayensa da kakanninsa. A wayi gari cewa ga wani Sarki ya warware abin da mahaifinsa ya yi, to gaskiya zai shafi mutuncin Masarautar."
"A gaskiya idan aka diba, an riga an san cewa idan dai wani sarki ya aiwatar da wani abu, idan wani ya zo ko bai yarda da wannan abin ba, ba ya komawa baya a kansa. Domin yana ganin cewa idan ya yi wani abu na daban da wanda ya gabata ya yi, to kamar tsirara ya yi wa wancan sarkin", in ji Dr Naniya.
A cewarsa, nadin sabon abu ne da aka kirkire shi a Masarautar Kano saboda "Masarautar Kano tana da matsayi na Sarkin Dawaki Mai Tuta, wato kujera ce babba (wadda) ke cikin wadanda za su iya shiga cikin nada sarki,"
"Abin da ya shafi Sarkin Dawaki babba, an kirkiro wata sabuwar sarauta ce daban a cikin Masarautar Kano wadda ba mu san gurbin da za a ba ta ba a nan gaba."
Dr Naniya ya kara da cewa wannan matakin wata hanya ce ta raunana Masarautar kuma "nan gaba ko da matsayin Masarautar ya dawo yadda yake, tarihi sai ya nuna irin wannan badakala da aka yi cewa ba ta yi wa masarauta dadi ba, ba ta yi wa sauran sarakuna na Daular Usmaniyya dadi ba.
"Domin bude hanya ce wadda nan gaba duk inda aka samu irin wannan za a kawo misali da Kano saboda haka hanya ce da za a raunata Daular Usmaniyya gaba daya da kuma irin tarihin da jihadin da Shehu Usmanu ya yi wajen nada sarakuna."

'Siyasa ta yi tasiri a lamarin'
Masanin ya kuma ce wannan ya nuna cewa siyasa ta yi tasiri a ciki sannan yana da illa domin yanzu "ya shigar da Masarautar cikin siyasa kuma duk wani gwamna da ya zo zai yi abin da ya ga dama kuma duk wanda yake so a nada a matsayi zai san ta hanyar da ya shiga ya fita, ko dai ya yi nasara ko ya cire sarkin da ya samu domin shi ma ya biya wa kansa bukata."
Dr Tijjani Naniya ya bayyana cewa hakan ya nuna cewa "duk rikicin da aka yi a kan sarauta tun lokacin Sarki Sunusi Lamido Sunusi na II [Muhammadu Sanusi na II ] wato duk rikicin da ya taso, wadansu mutane ne suka shiga sha'anin siyasa suka babbake domin su cimma buri."












