Tsige Sarki Sanusi, tarihi ne ya maimaita kansa

Asalin hoton, KASSIM TURAKI
- Marubuci, Daga Mahmud Jega
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai sharhi kan al'amura a Najeriya
Kusan dukkan masu sharhi sun yi hasashen faruwar wannan lamari, wato rikicin da ke tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi na II zai kai ga cire sarkin daga mukaminsa.
Sai dai duk da haka al'amarin ya zo wa mutane da dama da matukar mamaki in ban da na kurkusa da gwamnatin jihar.
Tun a 2019, Ganduje da gwamnatinsa karkashin jam'iyyar APC ba irin jafa'in da basu yi wa Sarki Sanusi II ba. Masu taimaka wa gwamnan da sauran wasu 'yan jam'iyyar sun yi ta sukar Sarkin karara.
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun yi ta rubuta korafe-korafe da dama a kansa, wasu lokutan ma wasu kungiyoyin sun yi ta sa hukumomi na bincikar ayyukan sarkin da masarautar.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano wacce "sarkin azarbabi" Muhuyi Magaji Rimin Gado ke shugabanta, ya jagoranci binciken ya kuma yi ta gayyatar manyan jami'an masarautar.
Hakazalika mambobin Majalisar Dokokin jihar inda mafi yawan su 'yan APC ne sun yi ta samun korafe-korafe, ciki har da korafin da suka samu a makon da ya gabata da ke zargin cewar ta sayar da wasu filayen masarautar.
Mafi girman kaskancin da aka yi wa Sarki Sanusi II shi ne na kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar a bara, da suka hada da Karaye da Bichi da Rano da kuma Gaya.
Hakan ya matukar rage karfin ikon da Sanusi yake da shi daga kasancewar masarautarsa mai kananan hukumomi 44 zuwa 10.
Akwai lokacin ma da gwamnatin ta yi kokarin mayar da matsayin Sarki Sanusi II da sunan Sarkin Birnin Kano, abin da ya taba kimar masarautar mai shekara 1,000 sosai.

To me ya jawo duk wannan rikicin?

Asalin hoton, Sani Maikatanga
Za a iya cewa abu biyu ne suka jawo hakan. Kasancewar sa marar ganin zarau sai ya tsinka, abin da ya matukar bambanta shi da mutumin da ya gada a 2014 Alhaji Ado Bayero.
A yayin da Ado Bayero ya kasance mai matukar dauke kai daga abubuwa da dama tare da sa wa bakinsa amawali a shekara 51 din da ya yi a karagar mulki, shi kuwa Sarki Sanusi II bakinsa ba ya iya yin shiru, inda duk tarukan da ya halarta sai ya bar abin fada.
A al'adar arewacin Najeriya, yawanci Sarki ya kan bayar da shawara ne kawai ya kuma yi addu'o'in zaman lafiya, amma Sarki Sanusi II ya zamanto mai jawabi a kusan duk taron da ya halarta.
Ba kamar yadda sauran sarakuna ke yi ba, ya kasance yana gabatar da dogwayen jawabai a wajen taruka, da musayar ra'ayi a ilimance, da ambato alkaluman Bankin Duniya da na gaggan masana tattalin arziki na yammacin duniya da masu ilimin falsafa da kuma Malaman Musulunci.
Salonsa ya bambanta da dukkan sarakunan arewacin Najeriya, wadanda yawancin su ba su faye yin magana a bainar jama'a ba.

Wani babban abu shi ne, Sarki Sanusi II ya rinka fitowa fili yana tsokaci kan wasu batutuwa wadanda masu sharhi kan lamuran yau da kullum ne kawai ke magana a kansu da gidajen jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu.
Akwai lokacin da ya ce Arewacin Najeriya na gudanar da Addinin musulunci tamkar a karni na 13 wanda hakan ya fusata manyan malamai a yankin.
Ya soki yadda talakawa ke auren mace fiye da daya kuma suna haihuwar 'ya'ya da dama, ya bayyana cewa irin wannan al'adar na durkusar da 'yan arewa.
Irin wadannan batutuwa na fitowa ne kadai daga bakin manyan masu ilimi da marubuta a gidajen jaridu, sai dai fitowar irin wadannan kalaman daga bakin sarki ya jawo ce-ce ku-ce daga bangarori da dama.
A farkon wannan shekara, Sarki Sanusi II ya bayyana cewa a kama iyayen da suka bar 'ya'yansu kara zube har aka yi garkuwa da su sakamakon nuna halin ko in kula sun bar su suna ta gararamba.
Ya kuma taba fitowa fili ya bayyana cewa Ganduje da kuma 'yan majalisa Kano sun shafe sama da wata daya a China suna neman a zuba jari kan layin dogo na jirigin kasa. Sun ce sun shafe kwanaki hudu ne kawai.
Ana ganin cewa kalaman da Sarki Sanusi II yake yi ya jawo masa kwarjini a kudancin Najeriya da kuma kafafen yada labarai na kudancin.

Asalin hoton, MASARUTARKANO/INSTAGRAM
A irin siyasar Najeriya mai cike da rudani, duk wani abu da yake da farin jini a kudancin Najeriya, ba lallai ba ne yana da shi a arewacin kasar ba, haka kuma abin da yake da farin jini a arewaci ba lallai ba ne yana da shi a kudanci.
Akwai matasa da dama 'yan arewacin Najeriya a shafukan sada zumunta da ke zargin cewa Sarki Sanusi II wanda ya yi makarantar Kings College ta Legas, na hada kai da 'yan kudu wajen musgunawa yankinsa na arewa.
Ana ganin cewa da a ce bai shiga siyasa ba da ba a tsige shi daga sarauta ba.
Gwamna Ganduje da kuma manyan jam'iyyar APC na ganin cewa tsohon sarkin yana goyon bayan PDP matuka inda suke zargin ya fitar da kudi wajen kamfe din Abba Kabir Yusuf a zaben 2015.
Ganduje da magoya bayansa ba su fito fili sun bayyana shaidarsu kan zargin da suke yi wa Sarki Sanusi II ba, amma ana ganin wasu makusantan sarkin ne suka kai labarin ga 'yan APC na Kano.
Amma ranar da ake ganin an samu baraka ita ce ranar da aka bayyana Ganduje a matsayin wanda ya ci zaben gwamna karo na biyu bayan zaben mazabar Gama a bara.
Daruruwan masu goyo bayan Gwamna Ganduje ne suka yi tururuwa suka afka gidan gwamnati suka saka tsani kuma suka kakkabo hoton Sarki Sanusi II wanda ke gidan gwamnatin.

Da bai shiga siyasa ba zai iya tsira
Duk da haka, da zai iya tsira da rawaninsa idan da bai sa kansa a siyasa ba.
Gwamna Ganduje da wasu shugabannnin APC sun yi imanin cewa jam'iyyar PDP Sarki Sanusi II ya mara wa baya, wasu ma cewa suke ya yi amfani da kudinsa domin taimaka wa yakin neman zaben dan takarar PDP Abba Kabir Yusuf Gida Gida a a zaben 2019.
Ba a san hujjojin da Ganduje da magoya bayansa suke da su ba kan Sarkin, amma kila sun samu bayanai daga 'yan siyasa har ma da wasu daga Fadar Sanusi.
Alamar farko ta rikicin ta fara ne ranar da aka sanar da Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara a zaben Gama da aka sake, inda daruruwan magoya bayansa suka dinga cire hotunan Sarki a bangon gidan gwamnati.
Tun barkewar rikici tsakanin Ganduje da tsohon sarkin a bara, wasu gwamnonin arewa da manyan sarakunan yankin karkashin jagorancin Sarkin Musulmi suka nisanta kansu.
A cewar daya daga cikin gwamnonin, saboda gwamnonin arewa da manyan sarakunan arewa sun samar da sulhu tsakanin bangarorin biyu a 2017 amma daga baya suka kwabe.
Sun daura wa Sarki Sanusi II laifin rushewar sulhun suna masu cewa ya saba yawancin sharuddan da aka shata kuma aka amince a taron sulhun da aka taba gudanarwa a Kaduna.
Makusantan Ganduje da masu ba shi shawara sun taka rawa a rikicin. Suna ganin kamata ya yi a tube Sarkin tun suna kan madafun iko domin zai iya masu illa lokacin da suka sauka.
A zahiri, a daren da gwamnoni suka jagoranci sulhu a 2017, Ganduje ya fuskanci bore daga wasu manyan makusantansa, wadanda suka zarge shi da mika wuya ga matsin lambar da suke fuskanta.
Wasunsu ma sun ce tun da har suna fuskantar mummunar adawa daga bangaren Kwankwasiyya, kamata ya yi su rage zafin hamayyar ta hanyar tube Sanusi.
Ga alama magoya bayan PDP sun kara dagula lamura ga Sanusi da suka dawo suna goyon bayansa. Duk lokacin da ya fito a bainar jama'a, matasa da Ganduje ke tunanin magoya bayan Kwankwasiyya ne ke dabaibaye motarsa (limousine).

Asalin hoton, Masarautar Kano
Kafin gwamnatin Kano ta tube Sanusi, wani kudiri a majalisar dokokin majalisar Kano da ke neman a tube Sarki ya haifar da hargitsi inda 'yan PDP a majalisar suka dauke sandar majalisar.
Don haka, ko da son rai ko babu, rikicin APC da PDP ne ya yi tasiri ga kai wa ga matakin tube Sanusi.
Ana kuma ganin Muhammadu Sanusi na biyu bai samu goyon bayan jagoran siyasar APC ba, Shugaba Muhammadu Buhari.

Sukar gwamnati
Tun daga shekarar 2015 Sarki Sanusi yake sukar tsarin tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Buhari ko kuma rashin daukar matakan tattalin arzilkin.
A wani lokaci ya ce bai kamata Najeriya ta fada rikicin tattalin arziki ba saboda faduwar farashin man fetur da a ce gwamnati ta dauki matakan da suka dace.
A kwanakin baya Gwamna Ganduje ya jagoranci wata tawagar manyan mutane daga Kano zuwa wurin Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja. Sai dai ba a hangi Sanusi a cikin tawagar ba.
A lokacin Buhari ya ce ba zai saka baki a rikicin ba saboda kundin tsarin mulkin Najeriuya na 1999 bai ba shi damar yin hakan ba - na saka baki cikin harkokin masararutun gargajiya.
Wannan maganar ta sace gwiwar dattawan arewa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar, wadanda suke kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu - da ake tunanin da sunan Buharin za su yi.
Da yawa daga cikin masu sharhi na ganin cewa wannan maganar ce ta bai wa Ganduje damar tsige Sanusi.
Karara take cewa tsigewar da aka yi wa sarki ranar Litinin wani yunkuri ne na hana kotu ta shiga tsakani da hukuncinta.
Tun a shekarar da ta gabata ne Sanusi ya rika samun hukunce-hukuncen kotu da ke hana a taba shi.
Wasu daga cikin hukunce-hukuncen an aikata su, ko kuma game da kirkirar sabbin masarautu, majalisar jihar ta sake duba dokar da ta yi, inda ta yi gyara kan dokar.

Dabarar Ganduje
Ba abin mamakai ba ne yadda Ganduje ya tsige Sanusi sannan ya yi sauri ya bayar da sanarwar nada sabon sarki kafin kotu ta shiga lamarin. Masu kula da al'amura sun tsammaci faruwar hakan.
Amincewar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi na karbar sarautar Bichi, duk da cewa 'yan uwansa sun gargade shi cewa bai kamata ya taimaka wurin kacaccala masarautar Kano ba, hakan ya dadada wa Ganduje, domin kuwa ya karfafa gwiwar gwamnan.
An saka masa da lada mai yawa. Duk da yanayin da Alhaji Aminu Ado ya zama sarkin, sarkin ka iya zama mai farin jini saboda wayewarsa da kuma kusancinsa ga mahaifinsa.
Bayan tsige shi ne kuma gwamnati ta aika 'yan sanda domin su fitar da shi daga gidan sarauta sannan su kai shi jihar Nasarawa, inda za a kai shi wani boyayyen wuri sannan a rage yawan zirga-zirgarsa.
Haka aka saba tun lokacin Turawan mulkin mallaka, yayin da suka sauke sarakuna daban-daban zuwa Lokoja babban birnin Jihar Kogi.
Ana sa ran Sanusi ba zai bi umarnin killacewar ba.
Jerin manyan sarakunan da aka taba tsigewa a arewa cikin shekara 25
- Muhammadu Sanusi II ya zama sarki na uku mai daraja ta daya da aka cire tun shekarar 1963
- Sultan Ibrahim Dasuki an cire shi ne a 1996
- An cire Sarkin Gwandu Almustafa Haruna Jokolo a 2005.

Hakan na nufin uku daga cikin manyan masarautun Arewa (ban da na daular Borno) an tsige su ne a cikin shekara 25 kacal.
Yayin da ake tsammanin Sanusi zai je kotu domin yin korafin cewa ba a bi doka ba wurin cire shi daga mukaminsa, babu tabbacin zai yi nasara ganin yadda Dasuki da Jokolo suka kare - ba tare da nasara ba.
Cire Sanusi daga sarauta maimaituwar tarihi ne.
Gwamnatin Yankin Arewa ta sauke Sarki Muhammadu Sanusi I (kakansa) a shekarar 1963 bisa binciken Muffet kan harkokin kudi na Masararutar Kano.
Kasancewar jikansa Muhammadu Sanusi II sarki bayan shekara 51 ta wanke iyalinsa. Yanzu kuma, masu camfi za su kalli tsige shi da aka yi a matsayin cewa rashin sa'a a jinin iyalin Sarki Sanusi na I yake.
Wasu na ganin tsigewar ka iya zamar wa Sanusi gobarar titi domin kuwa zai iya koma wa siyasa kuma ya yi takarar shugaban kasa a 2023. Abin jira a gani ne.
Zuwa yanzu, Ganduje da mukarrabansa dole ne su fara tunanin yadda za su kare abin da suka aikata - kamar karin masarautu hudu da suka kirkira a shekarar da ta gabata.
Sabon Sarki Aminu Ado Bayero ba zai so sabbin masarautun ba duk da cewa daga cikinsu ya fito. Za a zuba ido a gani ko za su rushe su.











