Kalubalen da ke gaban sabon Sarkin Kano

Masarauta

Asalin hoton, Instagram/Aminu Bayero

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da matakin gwamnatinsa na cire Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II daga gadon sarauta.

Kuma sa'oi bayan sanarwar, gwamnati ta bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano kuma sarki na 15 a tsatson Fulani.

Sai dai yayin da wasu ke goyon bayan matakin gwamnan, wasu kuwa gani suke matakin ya saba ka'ida.

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya nada Sarki Sanusi II kan karagar mulki ya dora alhakin tube sarkin kan Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan kalami na Kwankwaso ya sa fadar shugaban kasar mayar da martani inda ta tsame Shugaba Buhari daga lamarin tare da cewa batun cirewa ko nadin sarki abu ne da ya rataya kan wuyan gwamnatocin jihohi.

Tuni dai aka yi bikin mika takardar aiki da sandar girma ga sabon sarkin kuma masana na ganin akwai dunbin kalubale a tattare da sabon sarkin.

Dakta Tijjani Mohammad Naniya, masanin tarihi ne a a Jami'ar Bayero da ke Kano kuma ya shaida wa BBC wasu daga cikin kalubalen da ke gaban sabon sarkin.

Short presentational grey line

1. Yadda zai wanke kansa

Dakta Naniya ya ce babban kalubalen shi ne yadda zai iya jan hankalin mutane cewa ba ya cikin "wannan kutungwilar da aka shirya har wannan abu ya faru".

"Yadda zai nuna ya na kaunar fadar sarkin Kano abin da ya gada tun daga Dabo ya zuwa yanzu kuma ga shi ya na daga cikin wadanda suka yarda aka raba masarautar har ya karbi matsayin Sarkin Bichi."

"Yadda zai nunawa mutane cewar shi ba ya cikin kulle-kullen da aka yi ya ja hankalin mutane su yarda cewar tsakani da Allah kishin Kano yake yi da kuma masarautar." a cewar masanin.

Wannan layi ne

2. Dawo da hadin kan 'ya'yan sarki

A cewar Dakta Naniya, yadda zai iya dawo da hadin kan 'ya'yan sarki na masarautar Kano gaba daya - dukkan wadanda suka cancanta za a iya zabarsu musamman gidajen murabus wato na Sarki Muhammadu Sanusi I wanda shi ne Sarki Muhammadu Sanusi II ya gada na daga cikin kalubalen da zai fuskanta.

A ganinsa, wannan ya kawo baraka tsakanin gidajen biyu. Koda wasu sun goyi baya aka yi abin da aka yi amma yanzu akwai wadanda za su ga cewar abin da aka yi yanzu zai nisanta su daga sarauta gaba daya.

"Saboda abin da aka yi ya nuna cewar wani tsari ne wasu suka shirya -wanda sai gidan wani ne kadai zai yi mulki kuma hakan na da tsoratarwa a tsarin sarautar Kano,"

"Abin da aka yi a shekarar 1893 shi ne ya kawo basasa tsakanin 'ya'yan Sarki Abdullahi Maje Karofi da 'ya'yan dan uwansa Muhammad Bello,"

"Shi ne ya kawo gidan Maje Karofi ya kafa sarauta wanda har yanzu gidansa ne yake yi, gidan Bello ma an mance da shi,"

"Wannan abin idan aka kawo misali tsakanin gidan Ado Bayero da gidan Muhammadu Sanusi na I su ma sun shiga irin wannan, toh ba a san yadda makomarsu za ta kasance ba." kamar yadda ya fada.

Masanin ya ce ya kamata ya yi kokarin nuna cewar ba wannan ce manufarsa ba sannan idan aka zo raba sarautu, ka da ya nuna san kai dole ya rarraba ta duk inda wadanda suka cancanta domin a nuna musu cewar ba so ake a yashe su daga mulki ba.

Wannan layi ne

3. Janyo kowa a jika

Kalubale na uku da sabon sarkin zai fuskanta a cewar malamin jami'ar shi ne ya yi kokarin nuna wa jama'ar Kano cewa har yanzu gidan sarautar yana nan kuma domin su yake.

"Wannan zai samu ne ta yadda zai bijiro da kansa ga jama'a. Daman yana da farin jini tun lokacin mai martaba sarki mahaifinsa ya na da rai,"

"Har ma take ake masa 'Sai ka yi", Allah ya kawo ya yi din toh tunda Allah ya kawo ya yi ya nuna shi na kowa ne,"

"Ya bi hikimar da mahaifinsa ya yi. Ya janyo hannun 'yan kasuwa, ya janyo hannun samari, ya janyo hannun 'yan siyasa da 'yan boko ya shigo da su al'amuransa," in ji masanin.

A cewarsa, "Mai Martaba Sarki Ado Bayero da ya ga matsala ta na faruwa wajen 'yan siyasa lokacin Sabo Bakin Zuwo, ai kokari ya yi ya dauko dan uwan Aminu Kano ya ba shi matsayi na hakimi."

"Lokacin da aka kafa jamhuriya ta biyu da ba ta kasance ba lokacin Kabiru Ibrahim Gaya, ai dan uwan Kabiru Ibrahim Gaya shi ya dauko ya masa hakimi."

Ya kara da cewa "lokacin da Kwankwaso ya hau kan mulki ai dauko mahaifinsa ya yi ya ba shi matsayi."

Lokacin da Shekarau ya yi gwamna, ai dauko Shekarau ya yi ya ba shi Sardauna.

A cewar Naniya Marigayi Ado Bayero ya yi haka ne don ya tafi da 'yan siyasa saboda ya san cewa idan bai tafi da su ba ya san su ne za su yi kutungwilar karya sarauta.

"Saboda idan zai yi ya gane cewa siyasar ta yanzu da ta faru, ana rikici tsakanin Ganduje da mai gidansa na da Kwankwaso. Sai ya yi kokari ya nuna cewa shi na kowanne ne daga cikinsu."

"Idan ya yi kuskuren yin haka, toh makomar sarautar nan da shekaru toh za ta zama ta na rawa."

Ya ce sabon sarkin zai fuskanci babbar matsala matukar ya nuna inda ya karkata.

Shi kansa Gwamna Ganduje fahimtar da ya yi kenan shi ne ya dauka Sarki Muhammadu Sanusi II wata jam'iyya ko shugaban siyasa yake goyon baya wanda kuma ba sa shiri da gwamnan.

Yana daya daga cikin abin da ya kawo bita da kullin da aka yi ta yi.

Saboda haka idan ya bi wadannan kila zai rage matsalolin da za su taso masa ta yadda zai samu karbuwa.

Wannan layi ne

4. Dabbaka addini da kishin jama'a

Masanin ya ce ya kamata sabon sarkin ya tabbatar da cewa ya dabbaka abubuwan da aka gina masarautar a kai wajen sha'anin alkibla ta addini da kishin jama'a kamar yadda mahaifinsa ya yi.

"Mutanen Kano suna da ilimi suna da fahimta, nan da nan za su iya yi masa fassara su ga inda ya dosa, daga wannan sai ka fara jin guna-guni kuma guna-guni shi yake tada gutsiri tsoma," in ji sa.

Idan ya yi kokari ya yi wadannan zai samu sauki matuka.

Dakta Naniya ya saka ayar tambaya kan hujjar da aka yi amfani da ita wajen kasa masarautu gida biyar da aka yi.

Masarautun da ake da su a daular Usmaniyya sun karbo tuta ne daga Shehu, shi ya basu dama ake kiransu Amir.

"Su kuma wadancan da aka nada su saboda dalilai na siyasa, wa ya basu tuta? kuma wane tarihi suke karewa?"

Ya kara da cewa mutane za su so su ga yadda sarki zai nuna wa mutane shi sarki ne na Kano tsohuwar Kano wadda mahifinsa da kakanninsa shekara dubu baya suka rike.

''Yanzu an ce Kano kananan hukumomi da basu wuce takwas ba ita ce Kano kuma abin da talakawan Kano suke bakin ciki a kai kenan,'' inji shi.

Short presentational grey line