Sau nawa aka taba soke Hawan Sallah a Kano?

Ganduje

Asalin hoton, Kano Govt

    • Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Sanarwar da gwamnatin jihar Kano ta fitar na soke bukukuwan babbar sallah sakamakon annobar korona ba shakka ba za ta yi wa jama'a da dama dadi ba.

Bukukuwan Sallah musamman hawan dawakai na daga cikin abubuwan da ke kayatar da bikin sallah a kasar Hausa.

Annobar korona ita ce uzurin da gwamnati ta bayar na jingine bikin Sallah a bana domin tabbatar da cewa ba a yi cunkoson da zai sake yada cutar ba.

Ko a lokacin bikin karamar Sallah an hana bukukuwa da takaita cudanyar mutane saboda wannan annobar. Sannan an gindiya wasu sharuda don tabbatar da cewa mutane basu kamu ko sake yada annobar korona ba.

Tabbas soke hawan babbar sallah zai zo wa wasu mutanen Kano ba zata, kasancewar al'amura sun fara komawa kamar yadda aka saba, sannan kuma ana ganin cewa wannan ne karon karon farko da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai yi cikakken hawa tun bayan da ya zama sarkin Kano.

Dogarai

Ba wai masarautar Kano ce kadai za ta yi kewar hawan sallar ba, su ma sauran masarautun jihar da aka kirkiro za su yi matukar kewar hawan.

A bayyane take cewa Masarautun Rano da Karaye da Gaya da Bichi za su so gwamngwaje a lokacin bikin babbar sallar.

Sai dai jama'ar sabuwar masarautar Bichi su ma za su yi kewa kusan irin ta mutanen Kano, a lokacin karamar sallar 2019 ne kawai sarki ya taba yin hawa tun bayan kirkirar masarautar.

A bana masarautar ta yi sabon sarki Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda yake dan uwa ne ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da kuma yake da farin jini a wajen masu harkar sarauta.

Hawan sallah dai dadaddiyar al'ada ce inda sarakuna kan zagaye gari suna karbar gaisuwa daga jama'a a cikin wani yanayi na kade-kade da bushe-bushe da kuma annashuwa.

Jihar Kano na daga cikin jihohin da ke tarihin masarautar da ke wannann hawa, ana samun baki daga jihohi makwabfta da wasu yankunan nesa da ke zuwa Kano domin kallon hawa

Ko da yake wannan ba shi ne karon farko da ake soke hawan sallah ba sakamakon wasu dalilai.

Wannan layi ne
hawan salla a kano

Asalin hoton, NTDC Twitter

Tsakanin shekara ta 1981 zuwa 1983 an ta fuskantar kalubale wajen gudanar da hawan Sallah a zamanin mulkin marigayi Abubakar Rimi, saboda takun saka da yake yi da masarautar a lokacin.

Sai kuma a shekara ta 2012, inda Majalisar masarautar Kano ta soke bikin hawan sallah, wannan kusan shi ne karo na farko a cikin shekaru sama da dari biyu da aka soke hawan Sallar baki daya a Kano.

Majalisar, wadda ta bayar da sanarwar, ta ce an dakatar da bukukuwan hawan sallar ne saboda rashin lafiyar da Mai martaba sarkin na Kano Alhaji Ado Bayero ke fama da ita.

Sai dai duk da danganta soke hawan da rashin lafiyar sarkin, wasu na ganin kamar rashin jituwa ce tsakanin masarauta da gwamnatin Kano ta janyo aka soke hawan.

A shekara ta 2013 ma ba a yi hawan Sallah ba saboda dalilai na rashin lafiyar sarki, ba a dawo da bukukuwan hawa a Kano ba har sai shekara ta 2014 bayan rasuwar Mai martaba sarki Ado Bayero.

Bayan wannan lokaci wata shekara da aka sake Sallah ba tare da hawa ba ita ce shekara ta 2019 lokacin da gwamnatin Kano ta sanar da soke hawan Nasarawa, matakin dai ya sosa zukatan mutane musamman matasa da 'yan mata.

Hawan sallah

Asalin hoton, Manuel Toledo

Ko da yake gwamnati ta danganta dalilan tsaro a uzirinta, amma abu ne daya fito fili cewa ta dau wannan matakin ne sakamakon takkadama da ke tsakanin gwamnan Kano da fadar masarautar Kano. Hawan Daushe ne kawai ya samu yiwuwa shi ma kuma an gama an bar baya da kura.

Sai kuma a lokacin bikin karamar sallar 2020 da annobar korona ta kassara bukukuwan Sallah.

A wannan lokaci ma da al'umma ke ta shirin ganin an gwanje-gwanje a sallar layya, ganin yadda karamar sallah aka yi ta cikin dokar kulle, wata sanarwar da gwamnati ta fitar ta sanyaya guiwar kanawa, domin a wannan lokaci ma sa a sake sallar ne ba tare da bukukuwa ba.

Wannan layi ne