
Fadar mai martaba Sakin Kano
Majalisar masarautar Kano ta ce bana ba za a yi bukin hawan sallah kamar yadda aka saba yi a duk shekara ba.
Majalisar, wadda ta bayar da sanarwar, ta ce an dakatar da bukukuwan hawan sallar ne saboda rashin lafiyar da Mai martaba sarkin na Kano Alhaji Ado Bayero ke fama da ita.
Sai dai duk da danganta soke hawan da rashin lafiyar sarkin, wasu na ganin kamar dalilai ne na tsaro suka sa aka soke hawan.
Wannan dai shi ne karo na farko a cikin shekaru sama da dari biyu da aka soke hawan Sallar baki daya a Kano.
Ko a kwanakin baya masauratar Kano, ta bada sanarwar soke I'itikafi, irin ibadar nan da Musulmi kan kwashe kwanaki goma na karshe masalallai suna addu'o'i da nafiloli, domin neman wasu biyan bukatu daga Allah madaukakin sarki.
An dai hana I'itikafin ne a sakamakon dalilai na tsaro.
Birnin Kano ya yi fama da hare hare na bama-bamai da na 'yan bindiga a 'yan watannin da suka wuce, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Galibin hare haren, 'yan kungiyar Jama'atu Ahlil Sunna Lidda'awati , da aka fi sani da Boko Haram kanka yi ikirarin kai su.
















