'Yan jari bola a Ghana
Agbog-bloshie, wani juji ne a birnin Accra na Ghana, kuma wuri ne da ake hada-hadar karafan da aka yar.
Masu neman karafan kan kuma kona wayoyi, da fatan yin gamon-katar .
To amma kwararu sun yi amunnar cewa, yin hakan na da illa ga lafiyar jama'a.
Ga rahoton Bashir Sa'ad Abdullahi