Me Kano za ta yi da tallafin Naira biliyan 10 na CBN?

Gwamnatin jihar Kano ta samu tallafin Naira biliyan 10 daga babban bankin kasar CBN don farfado da kamfanoni da masana'antun da annobar korona ta naƙasa a jihar.
Darakta Janar ta hukumar lura da saka jari ta KanInvest a jihar, Hajiya Hama Ali Muhammad ce ta bayyana wa manema labarai haka a lokacin wani taron bita a kan shirin gudanar da wasu ayyukan jihar.
Ta ce burin hakan shi ne a ga yadda za a farfado da kamfanonin da annobar ta shafa don bunkasa tattalin arzikin jihar.
Tallafin kuɗaɗen sun shafi kamfanoni 50 da suka samu naƙasu sakamakon ɓarkewar annobar korona a ƙarƙashin ayyukan gwamnati na sake farfaɗo da masana'antu.
Hajiya Hama ta ce CBN ɗin ya amince ya tallafa wa wannan shiri da ƙarin wasu kuɗaɗe idan buƙatar hakan ta taso nan gaba.
"Za mu zauna mu tattauna da kamfanonin ɗaya bayan ɗaya, ba wai a tare ba. Ta wannan hanya ce za mu tattara bayanai game da matsalolin kamfanonin don mu ga yadda za a tallafa musu.''
Hukumar ta KanInvest da 'yan jihar mazauna kasashen waje, tare da haɗin guiwar ƙungiyar masu sarrafa kayayyaki ta Najeriya MAN ne suka yanke shawarar ɓullowa da wannan shiri don tallafa wa masana'antun da annobar ta shafa.
Hajiya Hama ta bayyana cewa hukumar ta samar da wani fom na nuna sha'awa ga kamfanonin, tare da sanar da cewa ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2021 ne wa'adin mika fom ɗin zai zo ƙarshe.
Ta kuma ƙara bayyana cewa ƙofa a buɗe take har ya zuwa lokacin da aka samu takardun neman guda 50.
"Ta nan ne za mu gano idan za su iya kashe Naira Biliyan 10 ɗin ko kuma akasin haka," a cewarta.
Shugaban ƙungiyar masu masana'antu na Najeriya, Malam Ahmed Mansur ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki da kada su yi ƙasa a gwuiwa wajen dawo da martabar jihar Kano da ta samu koma baya a ɓangaren harkokin ciniki da masana'antu.
"Wani bincike ya nuna cewa kusan kashi 50 bisa 100 na masana'antu a jihar Kano ko sun samu koma baya, ko kuma ma sun durƙushe baki ɗaya sakamakon annobar korona da sauran matsaloli,'' in ji shi.
Ya kuma ce ''Don haka, akwai bukatar haɗin guiwa ta yadda za a sake farfaɗo da masana'antu a jihar Kano, wanda hakan zai samar da ayyukan yi ga matasa da dama a jihar, tare da haifar da wanzuwar zaman lafiya.
Gwamnatin jihar Kano ta nuna jin daɗinta game da wannan yunkuri.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa ta sha ɓullo da tsare-tsare da nufin ɓunƙasa ƙananan masana'antu a jihar, sai dai ɓarkewar annobar korona a bara ta mayar da hannun agogo baya wajen cimma burin.
Kano dai ta yi suna a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya.











