Premier League: ‘Yan wasa uku kacal aka saya a watan Janairu

Yayin da ake shirin bankwana da watan Janairu, kawo yanzu 'yan wasa uku kacal aka saya a gasar Premier League ta bana.

'Yan kwallon sun hada da Robert Snodgrass da Andrew Lonergan da kuma Amad Diallo - su ne ukun daga cikin hudun da aka saya kai tsaye a Premier League kawo yanzu.

Ukun ma ba wasu fitattu ba ne, balle a ce an yi wata gagarumar sayayya a gasar mai farin jini.

Duk da surutai da aka ta yi a kan cinikayyar 'yan kwallo a Janairun, Aston Villa ce ta dauki Morgan Sanson daga Marseille da ta dau dan wasa gogagge da zai iya buga babbar gasa.

Kan wannan batun ba maganar 'yan wasan da aka dauka aro a watan Janairun nan ba, sai wadanda kungiyar ta saya ya zama mallakinta.

Me ya sa kungiyoyi suka kasa sayen 'yan kwallo a Janairun nan?

Tun farko masana na cewar watan Janairu lokaci ne da ake fuskantar kalubalen cinikayya.

Domin an shiga wata sabuwar shekarar da aka lissafi da kuma tsare-tsaren yadda za a tunkari gudanar da abubuwa domin samun riba.

Idan aka shiga watan Janairu an nutsa kenan a gasar nahiyoyin Turai, saboda haka kowacce kungiya kan rike fitattun 'yan was anta domin gani ta taka rawar gani a kakar ta tamaula.

Idan ka ji an dauki wani fitatcen dan kwallo sai dai idan ko ya tsufa bai da kwantiragi a hannunsa ko wanda keda sabani tsakaninsa da kulob dinsa da dai sauransu.

Haka kuma cutar korona ta jawo koma baya da kungiyoyi suka rage kasha kudade, bayan da ake buga wasa ba 'yan kallo.

Koma baya da cutar korona ta haddasa har da dokoki da kasashe suka gindaya wajen shiga kasarsu don gudun yada cutar korona.

Haka kuma bayan da Birtaniya ta fice daga kungiyar nahiyar Turai wato Brexit, akwai wato doka da ta kawo tarnaki.

Hukumar Turai ta kirkiri daraja 'yan wasan Turai da za a yi la'akari da kwarewarsa da matakin da yake sana'arsa ta tamaula kafin ciniki ya fada.

Ita kuwa dokar da takr Burtaniya ba batun daukar dan wasa daga wata nahiyar dan kasa da shekara 18, sannan kar su wuce uku masu shekara 21.

Burtaniya ta fice daga kungiyar Turai ranar 31 ga watan Disamba.

Wasu na ganin Brexit zai bai wa Burtaniya damar kara bunkasa 'yan wasan cikin gida da baki suka mamaye, saboda dole kungiya ta dauki matashi na gida ta kuma raina.